✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ziyarar gwamnonin APC ga Jonathan ta bar baya da kura

Jam'iyyar PDP ta ce ba komai bane yasa wasu gwamnonin APC suka kai wa Jonathan ziyara face gazawar iya mulki.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ziyarar da wasu gwamnonin APC suka kai wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ta nuna amincewarsu karara kan gazawar APC.

A ranar Asabar wasu gwamnonin APC karkashin jagorancin shugabanta na riko, Mai Mala Buni, sun ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja.

Sai dai ziyarar ta bar baya da kura, inda wasu a PDP ke ganin ta a matsayin yunkurin janyo tsohon shugaban kasar zuwa APC mai mulki.

Amma PDP ta bakin Sakataren Watsa Labaranta na kasa Kola Ologbondiyan ta ce ziyarar ba komai ba ce face nuna gazawar APC.

A martaninta ga PDP jam’iyyar APC ta bakin mataimakin sakatarenta ta ce PDP ta rude ne da ziyarar da gwamnonin suka kai.

Ya kara da cewa APC a matsayin jam’iyya za ta ci gaba da mayar da hankali ne ga abubuwan da za su kawo nasara da ci gaban Najeriya.