✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya dauki nauyin karatun marayun da Civilian JTF suka bari

A 2022 za a fara daukar nauyin karatun marayun ’yan sa-kai a yaki da ta'addnci tare da tallafa wa iyayensu a Jihar Borno

Gwamnatin Borno na shirin kaddamar da shirin Tallafin Jaruman Borno, domin daukar nauyin karatun marayun da iyayensu suka rasu a aikin sa-kan tsaro na Civilian JTF da sauransu a Jihar.

Shirin, mai suna “Borno Heroes Support Programme,” an bullo da shi ne domin tallafa wa matan aure da daukar nauyin karatun ’ya’yan da mafarauta da ’yan banga da kuma Civilian JTF da suka rasu a wurin yaki da kungiyar Boko Haram da ISWAP suka bari.

Gwamna Babagan Zulum ya ce, “Za mu bullo da shirin Borno Heroes Support Programme, wanda zai gano yara da shekarunsu bai wuce karatun firamare da sakandare ba, wandan ’yan Civilian JTF da mafarauta da suka rasu a bakin daga suka bari.”

Ya bayyana cewa a karkashin shirin wanda zai fara da marayu 500, Gwamnatin Jihar Borno za ta dauki nauyin karatunsu zuwa kwalejojin Gwamnatin Tarayya da ma na kasashen waje.

“Shirin zai kuma gano tare da tantance matan da wadannan jarumai suka bari, domin gwamnati ta rika ba su tallafin da ya dace na ci gaba da rayuwa”.

“Da dama daga cikin wadannan jarumai sun rasa rayukansu ne a kokarin ganin Jihar Borno ta samu zaman lafiya.

“Za mu yi musu sakayya ta hanyar ilimantar da marayu da suka bari tare da tallafa wa matansu a karkashin wannan shiri da za a kaddamar a watan Janairun 2022 idan Allah Ya yarda,” inji Gwamna Zulum

Da yake sanar da haka a lokacin da yake gabatar da kasafin 2022 na jihar a Maiduguri ranar Talata, gwamnan ya ce za a aiwatar da shirin ne a mataki-mataki.

Jihar Borno ta shafe shekara 12 tana fama ta matsalar ta’addancin kungiyar Boko Haram, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jami’an tsaro da ’yan sa-sai da da fararen hula, baya ga asarar dukiyoyi da tilasta miliyoyi yin hijira daga yankunansu.