✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya fatattaki kungiyar da aka gano tana ‘koya harbi’ a otal daga Borno

Umarnin ya biyo bayan bankado yadda kungiyar ke koya wa wasu harbi a otal.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya umarci a fatattaki wata kungiyar bayar da agaji ta kasa da daga Jihar ba tare da bata lokaci ba.

Umarnin ya biyo bayan bankado yadda kungiyar mai suna ‘ACTED’ ke fakewa da aikin bayar da agaji wajen koyawa wasu mutane harbi da bindiga a wani otal da ke Maiduguri babban birnin Jihar.

Kakakin Gwamnan, Malam Isa Gusau wanda ya sanar da umarnin ya ce an gano kungiyar ta kasar Faransa na amfani da bindigogin roba da makamantansu wajen horar da wasu mutane a otal din da ke kan titin Circular Road a Maiduguri.

Gusau ya ce makwabtan otal din ne suka jawo hankalin mahukunta a kan yawan jin karar bindiga da suke yi daga otal din a ko da yaushe.

Daga nan ne kuma aka kai rahoton ga Baturen ofishin ’yan sanda mafi kusa da ke unguwar GRA.

Gwamna Zulum ya kuma bayar da umarnin rufe otal din, tare da korar kungiyar ta ACTED daga kowanne irin aikin bada agaji a Jihar har zuwa lokacin da ’yan sanda za su kammala bincikensu.