✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya fi ni kwazo ta kowace fuska —Kashim Shettima

Shettima ya ce ya zabo Zulum ya gaje shi ne don share hawayen jama'ar Jihar Borno

Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa ya zabo Babagana Zulum ya gaje shi a jihar ne ba don kashin kansa ba sai dai don biyan bukatar jama’ar jihar Borno.

Kashim Shettima mai wakiltar jihar Borno ta tsakaiya a Majalisar Dattijai ya kara da cewa Zulum ya fi shi kwazo ta kowace fuska.

Tsohon Gwamnan Bornonn ya bayyana haka a yayin da yake gabatar da wata takarda a wani taro da gammayyar kungiyoyin matasa suka shirya a Birnin Kebbi mai taken “Rawar da jagororin Arewa za su taka wurin yi wa matasa jagoranci da bunkasa rayuwarsu”.

Da yake magana game da Zulum, Shettima ya bayyana magajin nasa a matsayin dan siyasa mai gaskiya da amana.

Ya kuma shawarci shugabanni da su tuna cewa, mulki dai na Allah ne, yana da wa’adi kuma kowa sai ya yi bayanin abun da ya aikata a gobe kiyama.