✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya mayar da yara 7,000 da Boko Haram ta raba da muhallansu makaranta

Wannan dai shi ne karo na uku da Gwamnan yake mayar da yaran jihar makaranta

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sa yara 4,229 wadanda yan ta’addan Boko Haram suka raba da gidajensu a Arewa maso Gabashin jihar zuwa makarantun Jihar daban-dabam. 

Yaran, wadanda suka fito daga kananan hukumomin Monguno da Kukawa da Guzamala da Marte, masu shekaru tsakanin shida zuwa 13, an shigar da su makarantun firamare da kananan sakandare ne.

A baya, rikicin Boko Haram ya tilasta musu tserewa tare da neman mafaka a garin Monguno na kimanin shekaru takwas.

Yayin kaddamar da wannan shiri na rijistar yaran a makarantu, Gwamna Zulum ya ce rajistar za ta shafi yara kimanin 7,000 ne.

“Yau muna nan a Monguno don manufa daya kacal, don sanya ’ya’yanku da rikicin Boko Haram ya hana su karatu sake mayar da su zuwa makarantu,” inji shi.

Gwamnan ya kuma yaba wa iyaye bisa dimbin jama’ar da suka fito don ba da ‘ya’yansu domin yin rijistar komawarsu makarantun.

Wannan dai shi ne karo na uku da gwamnatin Zulum ta shigar da yaran da suka rasa matsugunansu a garin Monguno zuwa makarantu don ci gaba da karatunsu kamar sauran yara.