✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya nada sabon Shehun Dikwa

Gwamna Babagana Umar Zulum na Jihar Borno, ya nada Abba Jato Umar a matsayin sabon Shehun Dikwa. Sanarwar nadin na kunshe cikin wata takarda mai…

Gwamna Babagana Umar Zulum na Jihar Borno, ya nada Abba Jato Umar a matsayin sabon Shehun Dikwa.

Sanarwar nadin na kunshe cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Gwamnan wacce ta ce za ta fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Janairu.

Nadin na zuwa ne bayan mako daya da rasuwar marigayi Shehun Dikwa, Alhaji Muhammad Ibn Masta El-Kanemi II wanda ya koma ga Mahallicinsa a ranar 23 ga watan Janairun 2021.

Marigayi Ibn Masta ya rasu ne bayan kwana guda da kai shi birnin Abuja.

Mutuwarsa ita ce ta uku ta jerin fitattun mutane a Jihar Borno cikin kankanin lokaci bayan ta Shehun Bama da ta Sarkin Biu a bara.

Sabon Shehun Dikwa, Abba Jato Umar