✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya raba wa tubabbun ’yan daba 152 tallafin N100m domin su ja jari

Gwamnan ya kuma dauki nauyin karatun yaran tubabbun matasan.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa tubabbun ’yan dabar siyasa su 152 tallafin Naira miliyan 100 domin su ja jari.

Yunkurin na ranar Juma’a ya biyo bayan horon wata daya da aka ba matasan, wadanda tsofaffin mambobin sananniyar kungiyar ’yan dabar nan mai suna ECOMOG ne da suka addabi Jihar, bayan sun tuba daga aikin nasu.

Gwamnan dai ya raba cakin kudaden ne a Kwalejin Fasaha ta Ramat Polytechnic da ke Maiduguri, wacce daya ce daga cikin wuraren da aka yi amfani da su don ba da horon.

Matasan dai sun bar ayyukan dabar ne biyo bayan haramta ayyukansu da Gwamnan ya yi a Jihar a shekarar 2019.

Wasu daga cikin tubabbun matasan
Wasu daga cikin tubabbun matasan

Bayan sanarwar dai a wancan lokacin, Gwamna Zulum a watan Agustan shekarar ya ba da umarnin daukar mutum 2,762 daga cikinsu aikin sharar kwatoci domin su rika samun kudaden kashewa.

Gamsuwa da yadda suka canza halayensu ne ya sa Gwamnan ya kuma ba da umarnin zabar mutum 152 mafiya himma a cikinsu domin a koya musu sana’o’i.

A yayin bikin rufe horarwar dai, Gwamnan ya ce za a ba 16 daga cikin fitattun tubabbun matasan Naira miliyan bibbiyu, yayin da ragowar 136 kuma kowannensu za a ba shi N500,000.

Sai dai ya ce tallafin an bayar da shi ne bisa yarjejeniyar cewa ba za su sake komawa ayyukan dabar ba, kuma za su biya rabin kudaden daga bisani.

Kazalika, Gwamnan ya kuma ce Jihar za ta dauki nauyin karatun yara 152, wanda kowanne daya daga cikin tubabbun matasan zai kawo.