✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya shammaci wasu malaman Firamare da jarabawar ba-zata

An yi jarabawar ne don a auna kwarewa da cancantarsu a fannin koyarwa.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya shammaci wasu malaman makarantar firamare da ke garin Baga da jarabawar ba-zata.

A cewar mai magana da yawunsa, Isa Gusau, Zulum ya yi wa malaman jarabawar ne don a auna kwarewa da cancantarsu a fannin koyarwa.

Gwamnam ya shammaci malaman ne a ranar Litinin yayin ziyarar aiki ta kwana daya da ya yi a garin na Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno.

Sanarwar ta ce, “Zulum ya fadawa malaman cewa, bai gudanar da jarabawar ba ne don a kori wani malami daga aiki, sai dai don a auna kwarewarsu don a san inda suka fi cancantar a saka su.”

A cewar Zulum, wadanda ba su da kwarewa a fannin koyarwar, za a ba su zabin a mayar da su wata ma’aikata ko kuma a tura su su karo ilimi.

“Zulum ya ce a karshen kowacce shekara, za a rika auna kwarewar kowane malami da dalibi, sannan gwamnati za ta tallafa masu da wurin zama da sauran ababen more rayuwa.”

Sanarwar ta kara da cewa, bayan da aka kammala jarawabar, gwamna Zulum ya sanar da ba da tallafin naira dubu 20 da yadin shadda goma-goma ga kowanne malami.

Kazalika, Zulum ya bai wa Shugabannin Makarantar tallafin naira dubu 50 da yadin shadda goma-goma.

“Muddin idan har za ku ba da gudunmuwar da za ta tallafa wa al’umma, za mu tallafa maku, za kuma mu rika yi maku jarabawa, sannan wadanda ya kamata a kara masu albashinsu za a kara masu,” in ji Zulum.