✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya tallafa wa manoma a garin Damasak

Ya ce tallafa wa manoman ita kadai ce hanyar farfado da harkar noma a Borno.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya raba tallafi ga manoma 1,200 da suka koma gidajensu a garin Damasak a Karamar Hukumar Mobbar.

Mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Gusau, ya ce a wannan yunkuri ne na farfado da harkar noma a Jihar, manoman sun samu tallafin taki, iri, sinadarin shuka, da kuma kudi 5,000 ga kowanne daga cikin manoman 1,200.

Mazauna garin, karkashin jagorancin Sanata Abubakar Kyari, sun yi alkawarin kara bunkasa harkar noma, don cika burin gwamnatin jihar.

Zulum ya ce tallafa wa manoman, ita ce hanya kadai da za a iya farfado da kalacewar harkar noma a Jihar.