✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya yi basaja, ya bankado yadda ma’aikatan asibiti ke tatsar marasa lafiya a Borno

Ya gano ma’aikatan na karbar tsakanin N8,000 da N10,000 daga marasa lafiya.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Alhamis ya yi basaja ya ziyarci wasu asibitocin gwamnati, inda ya gano yadda ma’aikatansu ke karbar kudade daga hannun marasa lafiya ba bisa ka’ida ba.

Ya gano cewa ma’aikatan asibitin na karbar tsakanin N8,000 da N10,000 daga hannun marasa lafiya, akan abubuwan da ya kamata su zama kyauta ne.

Gwamnan dai ya kira Kwamishiniyar Lafiya ta Jihar, Misis Juliana Bitrus, inda ya bukace ta su tafi tare, a wata mota mai cin mutum 10, wacce galibi suke amfani da ita wajen zuwa filin jirgi.

Daga nan ne kuma ya bar Gidan Gwamnati wajen misalin karfe 1:30 na rana ba tare da jiniya ba, lamarin da ya daure wa kowa kai.

Ya wuce kai tsaye zuwa wani sabon asibitin da gwamnatinsa ta gina kuma ta makare shi da kayan aiki a unguwar Gwange a birnin Maiduguri, inda ya iske wasu ma’aikatan wajen na karbar kudi kafin su duba marasa lafiya ga kananan cututtuka kamar Maleriya.

Hakan ta sa Gwamnan ya umarci Hukumar Kula Da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar da ta gudanar da zuzzurfan bincike a kan masu hannu a lamarin tare da daukar matakin da ya dace a kansu.

Zulum ya kuma nuna bacin ransa kan yadda ya iske ma’aikacin lafiya guda daya tilo a bakin aiki, duk kuwa da cewa akwai mutum 29 da suke aiki a asibitin.

Sai dai daga nan ya wuce wani makamancin asibitin da ke unguwar Gwange I, inda a nan kuma ya iske ma’aikata a bakin aiki, ba sa karbar kudi daga marasa lafiya.

Hakan tasa ya nuna farin cikinsa tare da yaba musu saboda kasancewarsu mutanen kirki.

Gwamna Zulum dai ya yi suna wajen kai ziyarar ba-zata a makarantu da asibitocin gwamnati a lokutan da ba a zata ba don tantance kwazon ma’aikata.