✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya yi rashin shugaban ma’aikata

Allah Ya yi wa Shugaban Ma’aikatan Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Babagana Wakil rasuwa a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli 2020. Mai magana…

Allah Ya yi wa Shugaban Ma’aikatan Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Babagana Wakil rasuwa a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli 2020.

Mai magana da yawun gwamnan Isa Gusau a cikin wata sanarwa ya ce za a yi jana’izar Babgana Wakil da karfe 4.00 na yamma a gidansu da ke Shehuri a garin Maiduguri.

“Allah Subhanahu wa Ta’ala, cikin rahamarSa, ya gararta masa kurakuransa Ya sa shi a aljanna sannan Ya ba iyalansa hakuri da dangana.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, inji Sanarwar.