✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum Ya Ziyarci ’Yan Gudun Hijirar Borno A Nijar

Mutanen da gwamnan ya ziyarta ’yan asalin garin Malam-Fatori ne, shalkwatar Karamar Hukumar Abadam da ke kusa da Tafkin Chadi wadanda ambaliyar ta raba da…

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci ’yan gudun hijirar da ambaliya ruwa ta raba da gidajensu da suka koma garin Bosso na Jamhuriyar Nijar da zama.

Mutanen da gwamnan ya ziyarta ’yan asalin garin Malam-Fatori ne, shalkwatar Karamar Hukumar Abadam da ke kusa da Tafkin Chadi wadanda ambaliyar ta raba da muhallansu.

Da yake jajanta musu, Zulum ya tabbatar musu cewa Gwamnatin Jihar Borno za ta taimaka wajen mayar da su garuruwansu da zarar ruwan da ke kwance ya janye, kowane lokaci daga yanzu, in Allah Ya yarda.

Ya gode wa Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum, wanda ya raka shi, da ’yan kasar bisa karimcinsu ga ’yan Jihar Borno, a duk lokacin da wani iftila’i ya afka musu.

Zulum ya ziyarci dakarun MNJTF

Gwamnan ya kuma ziyarci Rundunar Hadin Gwiwar Kasashe (MNJTF) da ke yaki da Boko Haram  da ISWAP — a kasashen Nijar, Chadi, Kamaru da Najeriya — inda ya yaba namijin kokarinsu a yaki da ’yan ta’addan suka addabi Yankin Tafkin Chadi da wasu kasashen.

Ya gode wa shugabannin kasashen bisa goyon bayansu wajen ganin an kawo karshen ta’addanci musamman ta hanyar tura dakarunsu fagen yaki.