✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun haramta bai wa ’yan gudun hijira agaji – Zulum

Gwamnatin jihar ta ce wannan yunkuri ne na gina rayuwar ’yan gudun hijirar a garuruwansu

Gwamnatin Borno ta haramta wa kungiyoyi masu aikin jin-kai bayar da agajin abinci ko wasu kayayyaki ga ’yan gudun hijirar da ke jihar.

Gwamna Babagana Zulum ne ya ayyana haramcin a wata wasika da ya aike wa kungiyoyin ta hannun Ofishin Kula da Ayyukan Jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ranar Laraba.

Wasikar ta bukaci masu aikin agajin da su mayar da hankali wajen bunkasa harkokin dogaro da kai tare da rufe bayar da tallafin kayan abinci.

“Kamar yadda kuka sani”, a cewar Gwamna Zulum, “Gwamnatin Jihar Borno ta kuduri aniya matuka gaya ta tallafa wa al’ummominmu su kasance masu juriya da dogaro da kai ta yadda za su raba kansu da talauci.

“Don haka ne Gwamnati ta kuduri aniyar rufe dukkan sansanonin ’yan gudun hijira da aka kafa a hukumance a Maiduguri a watan Disamba”.

Gwamnan ya kara da cewa shirin rufe sansanonin ’yan gudun hijirar ya kunshi taimaka wa jama’a su tsaya da kafafunsu.

“Wani bangare na wannan mataki shi ne karfafa wa mutane gwiwa su sake gina rayuwarsu.

“Sannan wani muhimmin tushe na wannan yunkuri shi ne yaye mutane daga dogaro da agajin abinci.

“Bugu da kari, wannan shiri ya kunshi maido wa mutane martabarsu da karfafa musu gwiwa su ci da guminsu, su kuma iya shata wa kansu makomar da ta dace da su”, inji wasikar.

Wasikar ta kuma ce wannan haramci ya shafi kungiyoyi na gida da na kasa-da-kasa.

Zulum, wanda ya ce a yanzu za a rika raba kayan agaji a sansanonin ’yan gudun hijira ne kawai da kuma ga ’yan gudun hijirar da ke cikin al’umma, ya bukaci kungiyoyin agaji da su nemi sahalewar Gwamnati kafin su yi haka don kauce wa cin karo da juna.

Zuwa yanzu dai Gwamnatin Jihar ta Borno ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira guda hudu a Maiduguri ta kuma sake tsugunar da mutanen da ke wuraren a garuruwansu na asali.