✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zuwa 2023 APC ta gama ruguza Najeriya —Hakeem Baba-Ahmed

Ya bayyana matsalar tsaro a matsayin gazawa a bangaren shugabanci.

Kungiyar Dattawan Arewa, ta yi zargin cewa nan da zuwa shekarar 2023, jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta karasa ruguza kasar.

Kakakin Kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ne bayyana hakan yayin hirarsa a shirin siyasa wanda gidan talabijin na Channels ya yada a ranar Litinin.

  1. Mutum 5 sun bace bayan fashewar sinadarai a Jamus
  2. ’Yan IPOB sun kashe DPO a mahaifar Gwamnan Imo

Baba-Ahmed, ya ce jam’iyyar da za ta karbi mulki daga hannun APC za ta gamu da babban kalubale.

Ya bayyana cewa matsalar tsaro da ake fama da ita a halin yanzu na da nasaba ne da gazawa a bangaren shugabanci.

Ya nanata cewar matsalolin da ake fuskanta a kasar sun zarta ta’addanci da satar mutane muni.

“Me za a yi da 2023 saboda daga yanzu zuwa 2023 APC ta gama lalata kasar nan gaba daya?

“Za ku ci gajiyar mulkin kasar a wargaje daga hannun jam’iyyar da PDP ce ta assasa ta.

“Saboda haka wane tanadi gare ku na gyara kasar nan kuma mene ne abin da kuke hasashen zai faru da Najeriya a 2023?” a cewarsa.

Bayanai sun ce a yanzu haka Najeriya na fuskantar matsalar tsaro mafi muni a tarihin kasar.