Zuwa ga Ministan Aikin Gona | Aminiya

Zuwa ga Ministan Aikin Gona

Salamun alaikum Edita. Don Allah ka isar min da sakona zuwa ga Ministan Aikin Gona Alhaji Sabo Nanono kan kalamin da ya fada wa duniya cewa, mutum zai iya sayen abincin Naira 30 har ya koshi. To wannan kalamin bai zo mana da mamaki ba, kasancewar kwance yake a gida ana tura masa bayani na rubutun biro amma bai gani da idonsa ba kan halin da talakan Najeriya yake shan wahala wajen neman abincin da zai ci a bakinsa.Ya kamata Shugaba Buhari idan har kana son ganin talakan kasarka cikin walwala to ka tsaya ka dubi wannan kalami na Ministan da ka nada bangaren noma ya kamata ka bincike shi. Daga karshe ina rokon Allah Ya ba mu jagorori nagari masu fadin gaskiyar halin da al’umma suke ciki amin.

Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi. 08062206733

 

Kira ga Gwamnatin Gombe

Assalamu alaikum Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya kan ta taimaka ta dawo mana da makarantar sakandaren kwana ta Karamar Hukumar Nafada (Gobernment College Nafada) wanda aka dakatar da ita a shekarar 2014 da sunan rikicin Boko Haram, duk da rikicin bai shafe mu sosai ba. Sa’annan jihohin Borno, Yobe, Adamawa wadanda rikicin ya fi kamari a can makarantu da dama suna karatu yadda ya dace. Da fatar gwamnatin jiharmu za ta yi dubi a kan wannan al’amarin kamar yadda Gwamna ya yi alkawari lokacin yakin neman zabe.

Daga Babangida Yusuf, Nafada Jihar Gombe. 08084618579

 

Najeriya kasarmu ta gado mai dadi!

Shugaba nagari shi ne mai kokarin gano matsalolin mabiyansa da kokarin samar musu mafita. Talakawa ku zamo masu biyayya da addu’a ga shugabanninku. Don Allah mu guji mummunar dabi’ar nan ta kwadayi da daukaka darajar “DAUDAR DUNIYA”.

Daga Usman Abdullahi Abuja 08062277369

 

Jinjina ga Gwamnatin Najeriya

Edita ba ni fili don girman Allah in yi godiya ga Gwamnatin Tarayyar mai albarka kan maido ’yan Najeriya gida daga Afirka ta Kudu. Kuma muna ba gwamnati shawara kan ta kori duk ’yan kasar Afrika ta Kudu mazauna Najeriya kuma ta kori duk wani kamfani mallakar Afirka ta Kudu kamar kamfanonin MTN da shagunan Shoprite da sauransu. Mun gode gwamnati muna tare da ke.

Daga Amiru Isah Bakori, 08084213547

Hannu daya ba ya daukar jinka

Jama’a ya kamata a duk inda muke mu rika taimaka wa jami’an tsaro wajen kurmata musu duk wata bakuwar fuskar da ba mu aminta da ita ba. Domin su yi bincike a kanta don daukar mataki. Ta haka ne zai sa su samu kwarin gwiwar yin aikinsu na samar da zaman lafiya a cikin nasara. Da fatar za mu ci gaba da taimaka musu yadda ya dace.

Daga Shugaban Kungiyar MURYAR JAMA’A, Haruna Muhammed Katsina, 07039205659

 

Ta’aziyyar Bashir Sama’ila

Assalamu alaikum. Mai girma Editan wannan Amintacciyar Jarida. Don Allah ka ba ni dama in aika da sakon ta’aziyyar kwararren dan jarida, dattijon kirki, mai taimakon jama’a da addini, wato Alhaji Bashir Sama’ila. Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da al’ummar Unguwar Alkali, Zariya. Ya Allah Ka jikansa Ka gafarta masa kura-kuransa Ka sanya shi cikin bayinKa salihai.

Daga M. Bello Abubakar, Karamar Hukumar Kalgo Jihar Kebbi, 07052257756

 

Tsokaci kan taron matsalar tsaro a Nijar

Salam Editan Aminiya. Ina son ka ba ni dama in yi tsokaci kan taron da aka yi kan matsalar tsaro da ke addabar kasashenmu. Allah Ya sa taron da aka yi a kasar Nijar kan sha’anin tsaron Najeriya da Jamhuriyyar Nijar, kwalliya ta biya kudin sabulu.

Daga Kasimu Aliyu Sardaunan Matasan Assada, 08073785412

 

Zuwa ga ‘yan sanda da sojojin Najeriya

Assalam Edita. Ina gaisuwa da fatar alheri. Allah Ya taimaka amin. Don Allah Edita ka isar min da sakona zuwa ga Rundunar ’ Yan sanda da Rundunar Sojin Najeriya kan abin da ya faru a Taraba. Kyaftin Tijjani Balarabe Ya Allah Ka fitar da shi daga wannan tuhuma da ake yi masa. Su kuma ’yan sandan da suka rasu Allah Ya jikansu da rahama, amin.

Daga Rabi’u Laman, Benin City Jihar Edo 08067653314

 

Jinjina ga Kwamishinan Ayyuka na Jigawa

Salam Editan Aminiya. Ina son ka ba ni dama a jaridarka mai fadar gaskiya in fadi ra’ayina kan dan kishin Jihar Jigawa kuma dan kishin Gumel na daya, wato Kwamishinan Ayyuka na jiharmu Injiniya Aminu Usman Gumel kan irin ayyukan da yake kawo wa garin Gumel. Edita ka zo Gumel ko wakilanka su ga irin ci gaban da Gumel ta samu ta hanyar Aminu Usman. Tunda aka kafa Gumel ban ga dan kishinta ba irin Aminu Aminnin Gwamna Badaru.

Daga Auwalu Datti Gumel Baban Zainab 09059126973

 

Mun yaba da kaddamar da manyan hanyoyi a Bauchi

Assalam Edita. Ka ba ni dama domin in taya al’ummar jiharmu ta Bauchi murnar kasancewa ranar Litinin 22-7-2019 da Mai girma Gwamnan Jihar, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kaddamar mana da manyan ayyukan hanyoyin da suka zama gagarabadau. Allah Ya taimake ka Ya ba ka ikon cika mana alkawari, amin.

Daga mai kaunar Jihar Bauchi Nasir Malami Sidi, Malam Goje, Bauchi 08036311157

 

Kira ga Gwamnatin Kano

Assalam Editan Aminiya. Ka ba ni fili in yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da Hukumar Makarantar Tsabta (School of  Hygiene) don  Allah a duba tsarin yadda wannan makaranta take dalibai na shan wahala. Wajen neman takardar shiga, in ka samu wajen yin rajista wahala. Karbar takardar biyan kudi ma da za ka biya rajista aiki ne. In ka gama wajen karbar sakamako sai ka ci wahala. Don Allah gwamnati da hukumar makarantar su gyara tsarin yadda ake tafiyar da aiki a makarantar. Wahalar ta yi yawa. Allah Ya sa a duba a gyara amin.

Daga Husaini Tsoho Imawa Kura, 08027911150

 

Kira ga Gwamna Aminu Masari

Edita ka ba ni fili a jaridar jama’a AMINIYA domin in yi kira ga Gwamna Aminu Masari kan kokarinsa na biyan hakkokin tsofaffin ma’aikata wato “GIRATUTI”. Kamar yadda ka yi kokari da taimakawa wajen biyan wadanda suka rasu, muke roko a taimaki masu rai su ma, a biya su na shekarar 20l8 da 20l9, ’yan jihar da ma na kananan hukumomi na shekararun 20l7, 20l8 da 20l9.

Daga 08064984507

 

Gwamnoni ku dauki darasi daga Afirka ta Kudu

Assalam Edita. Gwamnonin Najeriya ku dauki darasi daga Afirka ta Kudu a kan hana kananan hukumomi kudadensu. Domin wallahi rigar Buhari kuka shiga. Amma har so kuke ku yaga masa cunar riga. Ku sani “Abin da  ya ci  Doma, ba zai  kyale Awai ba.”

Daga Tukur  Maraya Shanono, Jihar Kano, 07032442923

 

Fatar alheri ga jaridar AMINIYA

Assalamu alaikum, zuwa ga Editan jaridar Aminiya, jaridar da ake wa lakabi da kotun talakan Najeriya. Ina murna da fatar alheri gare ku. Don Allah ku mika sakon gaisuwata ga Shugaba Buhari da fatar Allah Ya tsare shi daga dukkan makiyansa.

Daga Jamilu Gambo Takai, Abban  Khadijah, 08094571634

 

Ministoci a tuna da talakawa

Assalamu alaikum. Ina yi wa dukkan ministocin Najeriya fatar alheri kuma Allah Ya taya su riko tare da waiwayar baya da abin da talakawa muke kuka a kai da kuma durkushewar kamfanoninmu da sauransu.

Daga Isah Murtala Gamagira 08135419744.

 

Rushe masallaci

Allah Ya kare addinin Musulunci a dukkan kasashen duniya, amin. Ya kamata gwamnatin Najeriya ta hukunta duk wanda yake da hannu don rushe masallaci a Fatakwal.

Daga Rabi’u G. Baba Minjibir, Jihar kano 09064194588

 

Jama’ar Potiskum na bukatar wutar lantarki

Salam Editan Aminiya mai albarka. Don Allah ku isar min da sakona zuwa ga Shugaban Karamar Hukumar Potiskum Alhaji Abdulahi Adamu Bazuwa, kan ya taimaka ga Unguwar Bayan Carbs ta Arewa da wutar lantarki. Allah Ya ba shi ikon yin haka amin.

Daga Sa’eed Bin Adam. 08130827007

Kira ga ’yan Majalisar Tarayya

Kira ga ’yan Majalisar Dokoki ta Kasar nan biyu, cewa ya kamata kowace jiha ta ba da ma’aikata daidai hakkin wakilanta a cikin majalisa.

Daga Aminu Askoza, 08065416485