✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwan Buhari Kano a da, da yanzu

Ban san wani wanda farin jininsa ya tsiyaye kamar Shugaba Buhari ba.

A lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zo kamfe Jihar Kano a ranar 20 ga Janairun 2015, garin Kano ya tsaya cik; ’yan kasuwa sun yi fitar dango zuwa wajensa saboda tsananin kaunar da Kanawa suke masa.

Buhari ya dawo ziyarar aiki a ranar 6 ga Disamban 2017, bayan ya yi kimanin shekara biyu yana mulki kenan, kuma lokacin da tsadar rayuwa da wahalar man fetur suka fara hargitsa lissafin talakan da ya zabi Shugaba Buhari.

A wancan lokaci, kowa ya shaida taruwar al’umma tun daga taro shi Shugaba Buhari daga filin jirgi zuwa a tarurrukan da ya yi.

Don haka, a lokacin da ya dawo kamfe na shirin kakar zaben 2019 a neman wa’adinsa na biyu a ranar 31 ga Janairun 2019, babu shakka a wancan lokaci Shugaba Buhari ya samu taro da tarba ta ’yan siyasa ce kadai da jami’an tsaro da kadan daga cikin al’umma da suka rage tare da shi.

A ranar Alhamis, 15 ga wannan wata na Yuli, Shugaba Buhari ya zo bude aikin gadar shataletalen Dangi da kuma kafa harsashin aikin layin dogo na jirgin kasa da zai tashi daga nan Kano zuwa Kaduna.

Sai dai tabbas, da alamu masifar da talakawa suka shiga ciki a wannan lokaci ta sa talakawan ba su iya boye adawarsa da gwamnatin ba, musamman a wajen murnar zuwan Shugaba Buhari a wannan karon in aka kwatanta da ziyarceziyarcensa zuwa Kano a baya.

Mutane suna cikin fargabar rashin tsaro da talauci mara misaltuwa saboda lalacewar darajar Naira, tashin farashin man fetur, rufe boda da kuma karin haraji na kaso 50% da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Don haka nake ganin ban san wani wanda farin jininsa ya tsiyaye kamar Shugaba Buhari ba!

Wallahi a ranar Alhamis din ta makon jiya da ya Shugaban Buhari ya shigo Kano, saboda tsoron me zai je ya dawo, da kuma don a baiwa Buharin tsaro, don kare shi daga jifa, da tsoron kada a masa ihun “ba-ma-yi”.

A kan haka ne aka hana mutane bude shaguna a kan titin Zoo da duka titunan da ake tsammanin zai kai ya komo; kuma aka datse duka hanyoyin zuwa guraren da zai ziyarta.

Hakanan kuma tunda ba lallai mutan birni su daga masa hannu cikin murna ba, sai aka debo mutanen karkara mota-mota, aka raba musu dari biyar-biyar don su daga wa Buharin hannu tunda ana tsoron ’yan birnin.

Karshe kuma sai Buharin ya shigo ta sama wato a jirgin saman helikwafta kamar tsuntsu bayan an hana mutane walwala.

Duk da karin ’yan hayar barka da zuwa, in ka debe jami’an tsaro, to adadin mutanen bai fi karfin kirgar yaro dan ajin sharar fage shiga firamare ba.

Da yawa daga cikin mutanen Kano ba su ma san Shugaba Buhari ya zo Kano ba sai bayan da aka tare hanyoyi da bayan ya fita a ka ji labari.

Wannan alami ne da ke nuna gazawar Gwamnatin Buhari.

Babu shakka, duba da raguwar magoya bayansa, ba a nan Kano ba kadai ma, har da sauran jihohin kasar nan, lallai ya kamata ya gyara salon mulkinsa.

Tarihi yana cike da misalai da ke tabbatar da cewa, duk lokacin da masoyan mutum suka rinjayi adadin makiyansa, to babu shakka hali ko aikin mutumin karbabbe ne kuma abin yabawa.

Haka nan duk lokacin da mutum yake kara adadin makiya ko ’yan adawa, to lallai yana kan kuskure, ko aikinsa ba ya kyau.

Don haka, kamar yadda Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira a gare shi a lokacin da ya kai masa ziyara a fada, ni ma ina kara kira ga Gwamnatin Shugaba Buhari da ta nemo dabarun sassauta wa al’ummarta wannan tsadar rayuwa da aka samu kai a ciki.

Kuma a kara kokari wajen samar da tsaro, musamman a yankunanmu na nan Arewa, ko manoma za su samu dama su koma gona.

Mubarak Ibrahim Lawan ya rubuto wannan mukala daga Jihar Kano. Za a iya samunsa a lambar waya: 08065462182 ko imel: [email protected]