✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Dakatar da Ganduje: Kotu ta tsayar da ranar 27 ga Mayu

Wadanda suka shigar da karar na neman kotu ta yanke hukuncin dakatar da Ganduje na wucin gadi.

Wata babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 27 ga watan Mayu, 2024, domin fara sauraron kararraki guda uku kan dambarwar dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Mai shari’a Usman Malam Na’abba ne ya jagoranci zaman kotun bayan sauraron lauyoyin ɓangarorin biyu, sun sanya ranar da za a ci gaba da sauraren karar.

Bayan sauraren bukatun masu shigar da karar tare da yin tambayoyi wanda aka ƙi yarda a amsa a farko, bukatun masu karar na haɗin gwiwa ne da ƙalubalantar ikon kotun don gabatar da su da sauraren lamarin.

Masu shigar da karar, sun haɗa da: Haladu Gwanjo da Laminu Sani Barguma ta hannun lauyansu, Ibrahim Abdullahi Sa’ad sun shigar da kara mai lamba 13 a ranar 16 ga Afrilu wanda mai bukata na biyu ya goyi bayansu.

Wanda suka shigar da karar na neman kotu ta yanke hukuncin dakatar da Ganduje na wucin gadi.