✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kasuwa ya lalata ’yar shekara 8 a Kaduna

Mahaifiyar yarinyar ce ta kai wa jami'an tsaro korafi cewa wanda ake zargin ya yaudari ’yarta zuwa dakinsa sannan ya yi lalata da ita.

An tsare wani dan kasuwa a gidan yari kan zargin yi wata karamar yarinya mai shekaru takwas fyade a yankin Kafanchan dak e Jihar Kaduna.

Wata babbar kotun kwastomari ce ta ba da umarnin tsare dan kasuwan mai shekaru 32 a gidan yarin bayan an gurfanar shi a bisa zargin a ranar Talata.

Jami’in hukumar Sibil Difens (NSCDC) da ya gabatar da karar ya shaida wa Mai Shari’a Michael Bawa, cewa mahaifiyar yarinyar ce ta kawo kara ofishinsu cewa wanda ake zargin ya yaudari ’yarta zuwa dakinsa sannan ya yi lalata da ita.

Daga nan alkalin ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin, a kuma dage shari’ar zuwa ranar 19 ga wayan May 19.