✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin albashi da 35% bata lokaci ne —NLC

Ma'aikata sun ce hukumar da ta yi musu karin 35% na albashi ba ta da hukurmin yin hakan

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da karin albashin da Gwamnatin Tarayya tayi musu a masayin “bata lokaci.”

Aminiya ta ruwaito a daren Talata cewa gwamnatin ta yi wa ma’aikatanta karin kashi 25 zuwa 35 na albashinsu; ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa kashi 28.

Sanarwar da mai magana da yawun hukumar kula da albashi ta kasa (NSIWC), Emmanuel Njoku, ya fitar ta duk karin za su fara aiki ne daga watan Janairun 2024.

Njoku ya kuma shaida wa Aminiya cewa za a biya ma’aikatan cikon karin albashin na watannin da suka gabata.

Sanarwar karin ta fito ne sa’o’i kadan kafin Ranar Ma’aikata ta Duniya, wanda hakan ya sa ake ganin karin wani albishir ne ga ma’aikatan gwamnati.

Kazalik karin albashin da aka yi, yana daga cikin shawarwarin kwamitin mutum 37 daga gwamnati da yan kwadago da sauran masu ruwa da tsaki da gwamnati ta kafa kan karin albashi, karjashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikata, Bukar Goni Aji, a watan Janairu.

Sai dai, kungiyar NLC ta bakin mataimakin sakatarenta, Chris Onyeka, ya ce karin albashin da aka yi bata lokaci ne kawai domin hukumar ba ta da hukurmin kayyade mafi karancin albashi na kasa.

“Abin da suka ce sun yi bata lokaci ne, ba shi da amfani a wurinmu da wurin ma’aikatan gwamnati,” in ji Onyeka a ganawarsa da wakilimu.

Sai dai duk da cewa wakilinmu na samun karin bayani, jami’in na NLC ya ki kara cewa komai kan lamarin.

Mun yi kokarin samun karin bayani daga wasu manyan jami’an NLC da takwarorinsu na kungiyar ma’aikata (TUC) amma hakan bai samu ba a daren.

NLC da sauran kungiyoyin kwadago dai na kira ne da a sanya mafi karancin albashi ya zama wanda zai wadaci ma’aikaci, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa a kasar.

Sun bayyana cewa idan za a sa mafi karancin albashin, dole a yi la’akari da yadda farashin kayan masarufi suke tashi, musamman bayan janye tallafin mai da gwamnatin ta yi.

Ana iya tuna cewa kungiyar ma’aikatan jami’an sun kekashe kasa cewa ba za su amince da mafi karancin albashin da ya gaza Naira dubu 300 a wata ba.

A lokacin shirye-shiryen Ranar Ma’aikata dai shugaban TUC na kasa, Festus Osifo, ya ce bangarensu na kan tattauna da kwamitin George Akume kan karin albashi.

A cewarsa: “Da farko TUC ta gabatar da N447,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma daga bisani sun daidaita na da NLC don haka ya karu zuwa N615,000.

“Game da kwamitin da ke aikin sa mafi karancin albashin kuma, har yanzu bai kammala aikin ba…. da wuya a ranar 1 ga Mayu Gwamnati ta sanar da karinsa zuwa N500,000 da muke sa rai,” in ji Osifo.

Njoku ya bayyana cewa kwamitin da ya ba da shawarar, daban ne da wanda Sakataren Gwamnati, Sanata George ke jagoranta kan bukatun kungiyoyin kwadago kan albashi.

Wasu manyan jami’an gwamnati dai sun bayyana cewa an sanar da karin albashin ne domin guje wa abin kunya da ke iya faruwa a lokacin bikin zagayowar ranar ma’aikata.

Wani daga cikinsu ya bayyana cewa kungiyoyin kwadago sun yi niyyar yin amfani da ranar domin nuna wa shugabannin siyasa yatsa.

Daya daga cikinsu ya ce bangaren gwamtani da jami’an tsaro ya kasa samun ganin shugabannin kwadago domin tattaunawa da nufin dakile yiwuwar zanga-zanga.

A cewarsa, akwai yiwuwar da gangan shugabannin kungiyar suka boye domin kada bangaren gwamnatin ya samu shawo kansu kan abin da suka shirya.

Gabanin yanzu, wata majiyar ta bayyana cewa zaman da hukumomin tsaro da bangaren gwamnati karkashin jagorancin Akume, suka yi da ’yan kwadagon a ranar Juma’a ya tashi ne ba tare a an cin-ma wata kwakkwarn sakamako ba.

Daga Sagir Kano Saleh, Idowu Isamotu, Baba Martins, Abbas Jimoh (Abuja), Abdullateef Aliyu (Lagos), Hamisu Kabir Matazu (Maiduguri), Salim Ibrahim Umar (Kano), Mumini Abdulkareem (Ilorin), Magaji Isa Hunkuyi (Jalingo), Habibu Idris Gimba (Damaturu), Hassan Ibrahim (Bauchi), Hope Abah (Makurdi), Tosin Tope (Akure), Adenike Kafi (Ibadan) & Kelvin Meluwa (Asaba)