✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare fasto kan aikata fyade

Wata mata ta maka wani limamin coci a kotu kan zargin mata fyade

Wata kotun majistare ta tsare wani limamin coci a gidan yari kan laifin yi wa wata matashiya mai shekaru 22 fyade.

Babbar Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas ta tisa keyar Fasto Sunday Adewoye zuwa gidan yarin ne a ranar Talaa bayan an gurfanar da shi.

Dan sanda mai gabatar da karar, Insfekta Ayodele Adeosun, ya shaida wa alkali cewa a ranar 17 ga Afrilu, 2024 ne Fasto Adewoye ya zakke wa matar da karfin tsiya a garin na Badagry.

Hakan a cewarsa laifi ne a karkashin dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Legas.

Mai shari’a Patrick Adekomaiya ya ba da umarnin tsarewar ne bayan da ya ki sauraron rokon fasto  Adewoye, mai shekaru 45.

Daga nan kotun ta dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin samun shawara daga hukumar shari’a ta jihar.

(NAN).