✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanatoci sun yi rikici kan sauyin kujeru a zauren Majalisa

Sanata Sahabi Ya'u ya yi korafin canjin wajen zama wanda ya janyo ce-ce-ku-ce da nuna wa juna yatsa a tsakanin sanatoci

Tsarin wajen zama a zauren Majalisar Dattawa da aka yi a ranar Talata ya raba kan sanatoci a lokacin da suka koma zama a babban zauren majalisar bayan da aka jima ana gyara wa.

Idan an tuna cewa babban zauren majalisar ya daɗe ana yi masa gyare-gyare.

A lokacin, sanatocin suna aiki ne daga zauren taron na majalisar na wucin gadi.

Bayan kammala aikin gyaran ne suka koma zauren da aka gyara domin gudanar da harkokinsu, bayan sun shafe kusan kwanaki 40 suna hutu.

Rikicin dai ya faro ne a lokacin da Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya fara fitar da sunayen sanatocin da suka yi bikin zagayowar ranar haihuwarsu a lokacin hutun.

Musamman Sanata Sahabi Alhaji Ya’u, ya tashi daga kujerar da aka ware masa domin ya kai korafi ga shugaban masu rinjaye, Sanata Micheal Opeyemi Bamidele, cewa bai ji daɗin kujerar da aka ba shi ba.

Lamarin da ya yi korafin ya janyo kakkausar suka daga Bamidele, lamarin da ya kai ga sanatocin biyu sun yi musayar kalamai a cikin wani yanayi mara daɗi.

Hakan dai ya koma musayar yawu, sakamakon haka ya tilastawa sanatoci yin gaggawar shiga wani zama na sirri

A zaman da ake yi na cin karo da juna, Sanata Ya’u a fusace ya nuna wa Opeyemi yatsa, inda ya yi korafin cewa kujerar da aka ba shi bai dace ba, kasancewar shi babban sanata ne wanda ya rike babban mukami na mataimakin shugaban marasa rinjaye a lokacin majalisa ta 9.

Cacar bakin ta kara tsananta lokacin da Sanata Danjuma Goje ya shiga batun, ya kuma koka ga shugaban cewa manyan sanatoci ba su da wani matsayi a cikin dokar majalisa.

Amma Akpabio ya yi kira ga sanatocin da ke kewaye da shi, da su kwantar da hankali, bayan nan ya yi jawabin maraba ga ’yan majalisar.