✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Dan takarar Gwamnan LP a Jigawa ya koma APC

Dan takarar ya koma ne da dimbin magoya bayansa

Dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar LP, Abdullahi Tsoho, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Hadimin Gwamnan Jihar, Badaru Abubakar, Habibu Nuhu Kila ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce dan takarar ya dauki matakin ne bayan ya fahimci APC na da dukkan muradun da ake bukata wajen ciyar da Jihar gaba.

Nuhu Kila ya kuma ce tsohon dan takarar ya sha alwashin cewa shi da dimbin magoya bayansa za su yi aiki tukuru wajen ganin APC ta yi nasara a zaben mai zuwa.

Yayin da yake karbarsa a ofishinsa, Gwamna Badaru ya nuna godiyarsa kan sauya shekar dan takarar, inda ya yi alkawarin cewa da shi da mutanensa za su ci gajiyar duk wani amfai da sauran ’yan jam’iyya ke ci.