✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Manyan ‘yan siyasa 4 sun sha alwashin kawo karshen siyasar Fintiri

Bayan komawarsu APC, Nyako, Ribadu, Ngillari da Abbo sun yi alkawarin kwatar mulki daga hannun gwamnan Fintiri.

Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Adamawa ta sha alwashin kwatar mulkin a hannun PDP a zaben 2023.

Hakan ya fito ne daga bakin shugaban APC na jihar, Ibrahim Bilal a wajen taron hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar da ta gudanar.

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Sanata Abdulazeez Nyako, tsohon dan takarar gwamna Nuhu Ribadu, tsohon gwamnan jihar Bala Ngillari da Sanata Ishaku Abbo sun sha alwashin kwatar mulki daga hannun gwamna Ahmadu Fintiri a zabe mai zuwa.

Shugaban jam’iyyar ya bukaci hadin kan tsofaffi da sabbin ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar domin karbar mulki a 2023.

Bilal ya kara da cewa sabbin wanda suka dawo jam’iyyar ta APC suna da iko da dukkanin dama da sauran ‘ya’yan jam’iyyar ke da shi.

Sannan ya kara da cewa zaben mambobi da jam’iyyar za ta gudanar a watan Janairun 2021, kowa zai iya tsaya wa takarar gurbin da yake so.

Kazalika, ya bukaci dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar da su bayar da hadin kai tare da rikon sabbin wanda suka sauya sheka zuwa APC a matsayin uwa daya uba daya, domin a cewarsa ita ce hanya daya da zasu kai ga gaci.