2023: Masoyan Buhari sun goyi bayan takarar Kwankwaso | Aminiya

2023: Masoyan Buhari sun goyi bayan takarar Kwankwaso

    Abdullateef Aliyu da Abubakar Muhammad Usman

Kungiyar Magoya Bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bukaci Jam’iyyar APC ta hakura da gabatar da wani dan takara a zaben 2023.

Kungiyar mai rajin ganin dorewar tsare-tsaren Buhari, ta ce abin kunya APC ta tsayar da dan takarar a 2023 alhali gwamnatinta ta gaza samar da tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yaki da rashawa da ta yi alkawari.

Don haka ta bayyana goyon bayanta tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, inda ta bukaci APC da ta mara mishi baya a zaben na 2023.

A baya-bayan nan Kwankwaso ya koma Jam’iyyar NNPP, wacce a karkashinta ya yanki takardar takarar shugaban kasa a zaben da ke tafi.

Da yake jawabi ga manema labarai a Jihar Legas, kodinetan kungiyar na kasa, Injiniya Miftahu Aliyu Hassan, ya ce kungiyar da ke da rassa a jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja, ta yanke shawarar yin aiki domin ganin Kwankwaso ya zama shugaban kasa.

Miftahu, wanda dan takarar kujerar Majalisar Wakilai na nazabar Tarauni a Jihar Kano ne a 2019, ya ce APC za ta bai wa kanta kunya a 2023 idan ta tsayar da dan takarr shugaban kasa a zaben.

A cewarsa, jam’iyyar tasu ta riga gaza samar da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.