✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Ya kamata a bai wa PDP dama ta inganta al’amura —Makarfi

Ina da shakku kan ko zabe zai yiwu a wasu yankunan kasar a lokacin babban zaben 2023.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmed Muhammad Makarfi ya ce idan aka sake bai wa jam’iyyar PDP dama a zaben 2023, za su kyautata al’amura.

A yayin da Makarfi yake tattaunawa da BBC Hausa, ya bayyana manyan matsalolin da ke janyo wa Najeriya cikas ta fuskar ci gaban kasa da bunkasar tattalin arziki da inganta tsaro.

Tsohon Gwamnan, ya bayyana  cewa al’amura sun kara tabarbarwa a sakamakon matsalar tsaro da ta addabi kasar.

A cewarsa, matsalar tsaro ta fi kamari ne a yankin Arewa maso Gabashin kasar a lokacin da jam’iyyarsu ke mulki a 2015.

Sai dai ya yi ikirarin cewa sun fara daukar matakan shawo kan matsalar saboda har an gudanar da zabe a yankin.

Ya bayyana cewa, “a wannan lokacin ina da shakku kan ko zabe zai yiwu a wasu yankunan kasar a lokacin babban zaben 2023.

“Kalli yanzu yadda yankin Arewa maso Yammaci ya koma, haka al’amarin yake a yankin Arewa ta Tsakiya, haka idan aka je Kudancin kasar.

“A Najeriya, harkokin noma ma yana gagara, kasuwanci yana gagara da zumunci yana gagara kusan abubuwa da dama suna gagara,” in ji shi.