✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: ’Yan siyasa ne ke murde zabe ba mu ba – INEC

Kwamishinar ta ce harkar murdiyar zabe wannan sai 'yan siyasa amma ban da INEC.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce babu ruwanta da murdiyar zabe amma ’yan siyasa ne ke aikata hakan.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamishinar hukumar ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi, yayin ganawarta da manema labarai da kungiyoyi a jihar.

Ta ce, “INEC ba ta murdiyar zabe, ’yan siyasa ne ke aikata haka.”

Onyeka ta ce babu wata kafa da hukumar za ta bari wadda za ta ba da damar murdiyar zabe a 2023.

Ta kara da cewa, murde zabe a wannan karo abu ne mai wahalar gaske saboda kyakkyawan shirin da hukumar ta yi wa manyan zabukan 2023.

A cewarta, hukumar za ta yi iya yinta wajen tabbatar da sahihin zabe, kuma ba za ta bari kowane irin matsin lamba daga ko’ina ya yi tasiri a kanta ba.