A cikin wata 6 sai da na yi yaji sau 20 —Bazawara | Aminiya

A cikin wata 6 sai da na yi yaji sau 20 —Bazawara

    Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna

Hafsat Ismail bazawara ce mai shekara 21 da ke zaune a Unguwar Dosa a Jihar Kaduna, wacce aurenta ya mutu bayan wata shida kacal da aure.

Ta ce aure wani abu ne mai wuyar sha’ani amma nata ya hadu ne da cin zarafi da duka har sai da aka kwantar da ita a asibiti.

Ta ce cikin ’yan kwanaki da yin auren, wanda ta ce na soyayya ne, mijinta ya fara dukanta kan karamin laifi, inda har ta kai ga ta kusa rasa rayuwarta.

A cewar Hafsat, kafin rabuwarsu da ma akwai saki biyu a tsakaninsu, mijin ya karyata a kokarinsa na dawo da ita.

“A wannan karon ya sake ni ne a gaban shaidu. Na wahala a aurena, a cikin wata shida kacal sai da na yi yaji sau 20,” inji ta.

“An buga hatimin kotu a takardar sakin saboda maza wasu lokutan sukan dawo su ce wai ba su sake ki ba, musamman idan suka ji za ki sake aure,” inji ta.

A cewarta, duk da kasancewarta bazawara rayuwa sai a hankali domin ba haka ta zata ba.

Labarin Haftsat daya ne daga cikin miliyoyin aurarraki da ke mutuwa a Arewacin Najeriya.

Masu ruwa da tsaki a lamarin sun bayyana damuwarsu a kan wannan matsala ta sakin aure kamar sauran matsaloli na shan kwayoyi a tsakanin matasa da kuma karuwanci.

Aminiya ta tattauna da zaurawa a Jihar Kaduna da Zariya da Kano, inda ta gano cewa Arewacin Najeriya da Musulunci ya mamaye rayuwar duk wata mace akwai kalubale da zaurawa ke fuskanta.

Matsalolin Da Muke Fuskanta – Zaurawa

Yahanasu Sa’idu mai shekara 38 ce da ta yi aure sau hudu.

“Aurena na farko ya mutu ne bayan shekaru sha biyu. Ina da ’ya’ya shida da mijina na farko amma uku sun rasu.

“Na sake wani auren bayan shekara daya amma sai mijin ya rasu kuma muna da ’ya daya, wacce Allah Ya yi wa rasuwa,” inji ta a yayin zantawarta da Aminiya a gidansu da ke Kwangila, a Zariya.

— ‘An Sake Ni Bayan Kwana 40 Da Aure’

“Na yi wani auren amma bayan kwana 40 sai na fito kuma har yanzu ban san dalilin da ya sa mijina ya sake ni ba.

“Shi ma kuma bai bayyana a cikin takardar sakin da ya ba ni ba. Amma na rungumi kaddara.

“Na sake auren mijina na hudu a Karamar Hukumar Makarfi, shi ma mun rabu,” inji ta.

Yahanasu ta ce sun fara samun matsala ne a aurenta na hudu bayan ta yi ciki.

“Ta ce wai uwargidanta wacce ba ta haihu ba ta rika yin barazanar kona gidan amma da taimakon dangin mijinta sai suka mayar da ita wani daki daya, domin a samu zaman lafiya.

“Na kwashe kusan wata biyu ban sa mijina a ido ba. Na haifi jariri amma ’yan uwansa suka rika taimaka min har suna da aka yi amma shi ya yi watsi da mu,” inji ta.

A cewarta, bayan ta gaji da jiran shi sai ta kai kara kotun shari’a, inda aka nemo shi.

“Da farko ya shaida wa kotu cewa ba zai sake ni ba, domin yana son in dawo gidansa mu ci gaba da zama tare da matarsa ta farko.

“Ni kuma ina tsoron rayuwata da ta jaririna, hakan ya sa aka raba auren,” inji ta.

Bayan shekara bakwai Yahanasu wacce a yanzu ta zama malamar kiwon lafiya kuma take dinki, ta ce ita take daukar dawainiyar ’ya’yanta hudu.

“Dan autana ne kawai dansa. Bayan rabuwarmu da shi na bukaci ya rika ba ni kudin abincinsa.

“Da farko ya kokarta amma daga baya kuma sai ya daina bayarwa.

“A yau yaron ya kai shekara bakwai amma mahaifinsa bai san komai dangane da cin sa ko lafiyarsa da karatunsa ko tufafinsa ba,” inji ta.

Game da ’ya’yanta uku da ta haifa da mijinta na farko, Yuhanasu ta ce ba ta dade da aurar da ta fari ba.

Haka lamarin yake ga A’isha Alhassan wacce aurenta na shekara 18 ya kare shekara shida da suka wuce, inda a yanzu ita ke daukar dawainiyar ’ya’yanta hudu.

Ta ce suna zaune lafiya da mijinta har sai da ya yanke shawarar yin wani abu wanda ta ce ba za ta bayyana ko mene ne ba.

A yanzu haka ta ce ba ta samun taimako daga wurin tsohon mijin nata.

Sai dai ba kamar Yahanasu ba, ita A’isha an hana ta shigar da kara domin neman hakkinta saboda ’yan uwanta sun sa baki.

“Dan abin da nake samu a sana’ata shi nake daukar nauyin karatun ’ya’yana da koya masu sana’a.

“Iyayena sun ce tun da Allah Ya rufa min asiri zan iya daukar nauyin ’ya’yana kar in dogara da mahaifinsu.”

— ‘Mijina Ya Sake Ni Saboda Rashin Lafiyar Da Na Yi’

Adama Muhammad mai shekara 42, cikin ban tausayi ta tuna da irin bakar wahalar da ta sha a hannun tsohon mijinta.

Adama da ke sana’ar abinci, ta bayyana cikin hawaye yadda aurenta da wani mahauci ya kare lokacin da ta yi fama da wata rashin lafiya.

Matar wadda ke da ’ya’ya bakwai ta nuna yadda aka yaudare ta, aka wulakanta ta da zaluntarta a lokacin rashin lafiyarta.

A cewarta iyayenta sun yi matukar kokari wurin samar mata da maganin cutar da ta canza launin jikinta har tsawon shekara biyu.

A cewar Adama, tana cikin wannan rashin lafiya ce mijinta ya sake ta.

“Da farko mahaifina ya bukaci da in koma dakina tun da na fara samun sauki amma sai na roke shi da ya bari.

“Tun daga nan nake zaune babu aure duk kuwa da cewa mijina ya yi kokarin in koma.

“Yana raye a Kano. Mun rabu kusan shekara hudu ke nan, amma duk dawainiyar ’ya’yanmu bakwai ni nake dauka.

“Bai taba ba ni ko Naira 10 in sayi sabulun yara ba.”

Ana Mana Kallon Masu Zaman Kansu’

Hafsat bazawara ce mai shekara 21 da ke sayar da takalma a yanzu, wacce kuma ke son kwalliya.

Ta bayyana cewa babban kalubale da suke fuskanta shi ne zargin suna zaman kansu.

“Ina son kwalliya sosai amma wasu mutane ba sa son hakan.

“Ban sani ba ko kila saboda al’adarmu ce a nan Arewa.

“Wasu na daukar mu a matsayin masu zaman kansu. Da zarar na fita sai ki ji mutane na gulma cewa ga ta can ko ina za ta oho!

“Sannan idan na dawo gida duk gulmar ce za ki ji, wasu lokutan har nune suke maki,” inji Hafsat Ismail a lokacin da take bayyana irin kyama da ake nuna wa zawarawa.

“Mutane suna gaggawar zargin mu da cewa mu masu zaman kansu ne. Babu wanda ya damu ya san abin da kake yi domin taimaka wa kanki.

“Idan kuma kika samu manemi wasu makwabtan da wasu na kusan ne za su zagaya su fada masa ai ke yawo kike yi, ko su ce ai an sha sakin ki don haka ke ba macen aure ba ce,” inji ta.

A’isha Hassan bazawara ce da ke zaune a Unguwar Dosa da ke Kaduna, inda shekara shida ke nan da mutuwar aurenta, kuma ita ke daukar nauyin ’ya’yanta hudu, sannan ta kuma ce har yanzu ba ta yanke shawarar sake wani auren ba duk kuwa da cewa ba ta rasa manema ba.

Yanzu ’yar kasuwa ce duk da cewa takan hada da harkar siyasa, kusan a yanzu ta zama fitacciya a unguwar.

“Mu zawarawa ne amma ba karuwai ba,” inji ta da take mayar da martani a kan zancen nuna kyama da ake wa zawarawa a Arewacin kasar nan.

“Mutum zai fito neman ki da aure amma sai ki ga wasu a unguwa sun je sun sanar da shi cewa ai ke karuwa ce kuma an sha sakin ki.

“Mafi yawanci irin wadannan gulmace-gulmacen sukan fito ne daga wurin wadanda suka nuna suna son ki kika ce a’a.

“Abin da ya rage masu shi ne yada karya a kan ki,” inji ta.

— ‘Abin Da Ya Sa Ake Kiran Zawarawa Karuwai’

Zawarawan sun dora alhakin kyamar da ake nuna musu a kan al’ummar da ta fifita kalaman maza a kan na mata.

Sannan kuma al’ummar ta fifita auren ’yan mata a kan zawarawa.

Shugabar Kungiyar Zawarawa ta Jihar Kano, Hajiya Altine Abdullahi ta tabbatar da cewa wasu mazan na yin amfani da mata da ke fama da rashin kudi.

“Idan maza suka saki mace sukan yi watsi da su cikin talauci domin ciyar da kansu da kuma iyayansu.

“Duk matar da ta tsinci kanta a wannan hali me za ta yi? Ba kowace mace ce za ta ki ba.”

Ta kara da cewa maza da ke zargin mata da karuwanci su ne matsalar, domin mace ce aka saka aka kuma bar ta ta nemo wa kanta domin ciyar da ’ya’yanta ba kuma tare da ana taimakon ta ba.

“Sannan ba ta da wata sana’ar yi amma duk da haka an bar ta ta samo wa kanta da ’ya’yanta.

“Sannan kuma akasarinsu iyayensu talakawa ne ko kuma sun rasu sannan idan ta tunkari namiji ya taimaka mata sai ya ce zai taimaka mata idan ta ba shi wani abu.

“Sannan gobe sai shi namijin ya rika cewa ai karuwa ce.”

Hatta mata da mazansu suka rasu ma ba a bar su a baya ba, domin Ruqqaiya Haruna, mai sayar da kayan sanyi wacce mijinta ya rasu a shekarar 2005 ta ce akwai masu yi mata kallon karuwa a duk lokacin da ta fita zuwa wurin kasuwancinta.

“Akwai lokacin da za ki ji suna cewa wai mun fita mun dawo da kudi amma sai mu rika cewa wai kasuwanci muke yi.

“Amma tun da kin san zuciyarki tsarkakakkiya ce ba za ki mayar da hankali a kan irin wadannan maganganu ba,” inji ta.

— ‘Maza Ba Su Son Auren Mata Masu ’Ya’ya Da Yawa’

A cewarta, ba ta sake aure ba saboda abu ne mai wuya namiji ya auri mace mai ’ya’ya da yawa.

“Shi ya sa kawai na mayar da hankalina wurin kulawa da ’ya’yana domin tabbatar da sun sami ilimi inganttace,” inji ta.

Sake-Saken Aure Ya Karu

A Arewacin Najeriya Alkaluma daga kotun shari’a a Magajin Gari na Jihar Kaduna sun nuna a watan Oktoban da ya gabata, an samu kararrakin aure 30, wanda hakan na nuna alkaluman na iya fin na Jihar Kano da ke da yawan zawarawa kusan miliyan daya da dubu dari bakwai, a cewar Shugabar Kungiyar Zawarawa Altine Abdullahi.

A shekarar 2009 zawarawa sun bukaci a yi dokar da za ta rika tilasta wa maza biyan su wasu kudade.

Haka nan matan sun yi barazanar yin zangazanga domin nuna rashin amincewarsu da yawan sakin aure da ake yi.

— Akwai Bukatar Dokar Aure —Shikh Aminu Daurawa

Sheikh Muhammad Aminu Daurawa ya goyi bayan samar da dokar da za ta kawo karshen mace-mace aure kamar yadda Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya nemi a yi.

“Za mu yi la’akari ne da dokar ma’aurata ta kasar Moroko da suke kira Mudawwana, wadda ke duba yadda ake aure tare da yin saki da karin aure da gado da kula da ’ya’ya,” inji ji shi.

Daurawa ya ce, “Duk aure ana ba da takardar shaida, ana ba da takardar saki da ke dauke da sa hannun shaidu kamar yadda ake yi a aure.

“Muna bukatar dokar ma’aurata da za ta rika saita al’amuran aure idan kuwa ba mu yi hakan ba, za a samar mana da na Turawa,” inji Daurawa.

Da take bayani a kan mahimmancin dokar, Shugabar Zawarawan ta ce, “Ba cewa muke yi kada a yi saki ba, domin Allah Ya halalta saki.

“Abin da ba mu so shi ne yadda ake wulakanta saki. A mayar da saki ya yi wahala. Saboda idan miji ya lura akwai hakkokin da doka ta dora masa a kan tsohuwar matarsa zai yi tunani kafin ya furta sakin,” inji ta.

Shirin Aurar Da Zawarawa Da Matsalolin Da Ya Haifar

“Ba za mu iya cewa an samu nasara dari bisa dari ba, amma kashi tamanin cikin dari an yi nasara, kashi 20 an samu matsala,” inji Sheikh Daurawa da yake amsa tambaya a kan ko shirin ya samu nasara.

Bincike ya nuna cewa akalla mata dubu biyu ne aka daura wa aure a cikin shirin daga shekarar 2012 zuwa 2017.

Shirin ya yadu har zuwa jihohin Kaduna da Gombe da Katsina da Sakkwato, inda akalla aka daura aure 3,211.

A cewar Hajiya Altine shirin ya taimaka wa zaurawa sun sami sababbin gidaje da kuma tattalin arziki amma dai ta ce shirin aurar da zawarawan kadai ba zai iya kawar da matsalar yawaitar sakin aure ba a Arewacin Najeriya.

Hukumar Hisbah wadde ke kan gaba wajen shirya irin wadannan aurarraki ta ce suna nan suna bibiyar aurarraki da aka daura kuma suna ba da shawarwari inda suka lura akwai kalubale.

Shugaban Hukumar a yanzu, Dokta Haruna Muhammad Ibn Sina ya ce yawaitar sakin aure na daga cikin abin da ke janyo sauran matsaloli cikin al’umma, musamman lalacewar tarbiyar matasa.

Ya ce saboda nasarorin da shirin aurar da zawarawa ya samu a yanzu haka hukumar na shirin shirya wani auren kuma har sun sami akalla wadanda suka nuna sha’awa kusan 300.

— Makarantar zamantakewar aure

Sheikh Daurawa ya kafa makaranta da nufin wayar wa da ma’aurata kai da masu neman aure.

“Dole ma’aurata su nemi ilimin zaman aure. Akwai bukatar sanin dalilin yin aure da nauyin da ya rataya wuyansu.

“Sannan idan auren ya mutu sai kuma su san hakkin kowannensu,” inji malamin.

A kwanakin baya malamin ya kirkiro wata manhaja ta ma’aurata mai suna “Auratayya” wadda a yanzu haka akalla mutum dubu goma ne suka sauke ta a wayayoyinsu na salula.

Za a nuna shiri na musamman kan wannan labarin a Talabijin din Trust TV a tasah ta 164 a Startime.