✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina tsangwamar masu sanya hijabi a Najeriya —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmin ya ce yin hakan ne kawai zai tabbatar da ’yancinsu na yin addini.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci a daina tsangwamar mata masu sanya hijabi a Najeriya.

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce yin hakan ne kawai zai tabbatar da ’yancin matan na yin addini kamar yadda doka ta tanada.

Ya yi wannan jawabin ne ranar Talata a Birnin Kebbi yayin zaman jin ra’ayin jama’a kan yi wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kwaskwarima da Majalisar Wakilai ta shirya wa masu ruwa da tsaki daga jihohin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara.

Ya ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne kowa ya yi addininsa. Allah Ya halicce mu ne domin mu bauta masa, saboda haka ya zama wajibi a kiyaye wa Musulmi wadannan hakkokin nasu a cikin kowace irin doka da za a yi.

“Na yi amanna cewa babu wanda zai hana ni gudanar da addinina kamar yadda ya kamata.

“Akwai wurare da dama da aka samu rahotannin hana wasu mata Musulmi sanya hijabi a makarantu. Ta yaya sanya hijabi zai zama matsala ga wadanda ba sa sakawa?

“Kamata ya yi ma mu karfafa gwiwar mabiya wasu addinan su yi abin da addinan nasu suka tanada, ta haka ne kawai za mu iya zama lafiya,” inji shi.

Daga nan sai Sarkin Musulmin ya yi kira da a kara karfafa gwiwar girmamawa da kuma mutunta addinai a cikin sabon Kundin Tsarin Mulkin.

Da yake nasa tsokacin, shugaban kwamitin Majalisar Wakilan, Adekoya Adesegun Abdulmajid ya ce tun 1999 ake ta kiraye-kirayen ganin an sake fasalin kundin bisa hujjar cewa sojoji ne suka tsara shi ba tare da la’akari da bukatun ’yan Najeriya ba.