✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko WHO na yin taro kan maganin gargajiya

Hukumar lafiya ta duniya na taron farko kan maganin gargajiya don ba da damar amfani da shi ba tare da ya illata mutane ba

A karon farko Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fara taro kan maganin gargajiya, inda ta ce tana kokarin tattara bayanai ne domin ba da damar yin amfani da shi ba tare da ya illatar da mutane ba.

Taron na kwanaki biyu, na gudana ne lokaci guda da taron ministocin lafiyar kasashen G20 a birnin Gandhinagar na kasar India.

A jawabin shugaban hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus na bude taron, ya ce taron zai taimaka wajen tattara alkaluma da hujjojin da suka kamata, wadanda za su bai wa hukumar damar amincewa don yin amfani da maganin gargajiya.

Shugaban majalisar kimiya ta hukumar Harold Varmus, ya shaida wa taron cewar dole ne suyi duba kan lamarin, musamman yadda a yanzu ake amfani da magungunan gargajiya, don gano masu inganci a cikinsu.

Duk da yadda ake amfani da maganin gargajiya a sassa da dama na duniya, amma kuma maganin na fuskantar suka daga bangarori daban-daban, musamman kan rashin samar da hukumomin da za su rika sanya wa bangaren ido.

Daga cikin kasashe 194 da ke karkashin hukumar ta WHO, kasashe 170 sun amince da amfani da maganin gargajiya tun a shekarar 2018, amma sai dai kasashe 124 ne kadai suka samar da dokokin amfani da maganin a kasashensu.