✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika dandake masu yi wa yara fyade —Sarkin Pindiga

Ya ce fara aiwatar da dokar za ta zama gargadi ga duk mai niyyar aikatawa

Sarkin Pindiga da ke Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Mohammad Seyoji, ya bukaci gwamnati ta yi dokar da za ta sa a fara dandake mazan da suka yi wa kananan yara fyade.

Sarkin ya ce yana jin takaicin yadda mutane suke nuna rashin imani da tausayi wajen yin lalata da kananan yara suna yi musu fyade wani lokaci su ji musu raunin da ka iya jefa rayuwarsu a mummunan yanayi.

Sakin ya bayyana haka ne a garin Kumo hedikwatar Karamar Hukumar Akko, lokacin da yake jawabi a wajen bikin ba da tallafin karatu da Gidauniyar Adda Girl Education Foundation da tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Tarayya, Mai shari’a Zainab Bulkachuwa ta bai wa yara 50 ’yan asalin Karamar Hukumar Akko.

Ya ce bai san yaran da suke zuwa barema da wadanda suke talla a tsakanin leburori, musamman a irin wuraren hakar ma’adinai da tashoshin mota cin zarafin yana kai wa haka ba.

Sarki Seyoji, ya yi kira ga Majalisar Dokoki da Gwamnatin Jihar Gombe ta bullo da wata doka kuma a aiwatar da ita cikin gaggawa ta fara dandake duk wanda aka kama ya yi wa yara kanana fyade.

Daga nan sai ya ce fara aiwatar da dokar dandakewar za ta zama gargadi ga duk mai niyyar aikata irin wannan mummunar dabi’a.