✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi wa Fulani makiyaya uzuri kan wa’adin sauya kudi – Miyetti-Allah

Kungiyar ta ce mambobinta na bukatar karin wa'adi

Kungiyar Kare Muradun Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta bukaci tsari na musamman ga al’ummarta kan wa’adin sauya takardun kudi na Naira da aka sanar da wa’adin sauyawa.

Jagoran kungiyar Alhaji Abdullahi Bello Bodejo wanda ya bayyana bukatar a yayin taron ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin, ya ce duk da kwamitoci da kungiyar ta kafa don wayarwa jama’arta kan lamarin, ya ce a al’umarsu za ta iya fadawa matsalar ’yan damfara idan ba a yi mata tanadi na musamman ba.

“Bafulatani ne zai sayar da shanu kamar talatin, amma sai ya ce sai dai abiya shi da ruwan kudi kasancewar shi kansa a haka zai biya wasu kudin dabbobin tun a kasuwar, sannan idan da ragowar kudi ya sa a leda ya wuce da su ruga da ke cikin jeji inda babu banki babu layin sadarwa, inji shi.

Shugaban na Miyetti ya ce kungiyarsu na goyon bayan tsarin sauya kudin matukar zai taimaka a kan inganta tattalin arzikin kasa.

“Bukatar da muke da ita ita ce a kara wa’adin zuwa kamar a kalla wata 6. kasashe irin Saudiyya sun sauya kudi a lokuta daban-daban, amma har yanzu suna amfani da kudaden kamar yadda mahajjata da su kan lamarin suke gani.

“Bayan samun labarin sauya kudin mun kafa kwamitocin wayar da kai a kan lamarin, kuma mu na fata a bangarenta ita gwamnati za ta duba yiwuyar kara wa’adin lokaci da kum yi wa Fulani makiya da sauran mazauna wurare irin nasu, tanadi na musamman a kai, inji shi.

Kungiyar wadda ta yi taron shugabanninta na jihohi a ranar ta kuma yi zargin kashe jama’arta musamman a jihohin Taraba da Benuwei.

Ya ce a Jihar Benuwei kuma ana fakewa ne da dokar hana kiwo ana musgunawa makiyaya wasu a tsaresu wasu a kashe, sannan a yi gwanjon dabbobinsu, kamar yadda kungiyar ta yi zargi.

Kungiyar ta Miyetti Allah ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kirkiro ma’aikata ta musamman don kula da sha’anin makiyaya da zai hada da kiwo da kuma karantarwa, sannan ta farfado da wuraren kiwo a matsayin hanyar magance masu matsaloli da suke fama da su.