✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A zartar wa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama’a —Aisha Buhari

Ina goyon bayan da’awar da Malam Abdallah Gadon Kaya ya yi.

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayyana goyon baya a kan kiraye-kirayen da ake yi na zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a ga mutumin nan da ake zargi da kashe daliba ’yar shekara biyar a Jihar Kano. 

Ana dai zargin Abdulmalik Tanko, mammalakin makarantar Noble Kids Academy da ke Unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nasarawan Jihar Kano kan kisan wata dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar.

A makon jiya ne aka gano gawar Hanifa wadda ake zargin Abdulmalik Tanko, ya sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

A yayin da aka gabatar da shi ga manema labarai, ya ce ya kashe ta ne bayan ya sanya mata shinkafar-bera a cikin shayi sannan ya gididdiba gawarta ya binne a wani rami da ya haka a makarantar.

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin jama’a inda aka rika yin alla-wadai da tofin Allah tsine a kansa da wadanda suka taimaka masa.

A wani bidiyo da a yanzu ya karade dandalan sada zumunta, wani fitaccen malamin addinin Islama a Kano, Malam Abdallah Gadon Kaya, a daya daga cikin karatuttukansa ya yi kira da a zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a kan Abdulmalik Tanko ta irin hanyar da ya kashe dalibar tasa Hanifa.

Malam Abdallah ya yi da’awar cewa, a kashe mutumin a bainar jama’a domin hakan zai zama izina ga kowa, lamarin da ya ce umarni kawai Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano za su bayar kuma aikin gama ya gama.

Ita ma uwargidan shugaban kasar ta wallafa wannan bidiyo na Malam Abdallah a shafinta na Instagram, inda ta bayyana goyon baya dari bisa dari a kan wannan kira.

A sakon da Aisha ta wallafa, ta ce “muna goyon bayan da’awar da Malam ya yi.”

Tuni dai Gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantar sannan ta sha alwashin hukunta mutumin da ake zargi da kisa kisan yarinyar.