✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da Buhari ya ce wa fasinjojin jirgin kasan da ’yan bindiga suka sako

"Damuwata yanzu ita ce yadda za a saki sauran fasinjojin lafiya ba tare da lahanta kowanne ba," in ji Buhari.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yana sane da sauran fasinjoji jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna 31 da har yanzu suke hannun ’yan bindiga.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ganawarsa da wakilan fasinjojin da aka sako a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Kakakin shugaban, Femi Adeshina, ya ce tun bayan faruwar lamarin gwamnati ta fara daukar matakai domin tallafa wa iyalan da abin ya shafa da kuma tabbatar da hakan ba ta sake faruwa ba a kasar baki daya.

Ya  kuma shaida musu cewa gwamnatin na yin duk mai yiwuwa domin ganin an dawo da sauran fasinjojin da har yanzu ke hannun ’yan bindiga.

“An sanar da ni cewa akwai ragowar fasinjoji 31 a hannun masu satar mutanen kuma mun maida hankali kacokan yanzu kan yadda za mu dawo da su ga iyalansu.

“Mun sami shawarwari game da amfani da karfin soja wajen yin hakan, kuma mun  zauna mun yi nazari kan hakan.

“Sai dai mun tabbatar ba zai bada nasarar da ake so ba, hakan ne ya sanya muka jingine matakin ba don son ranmu ba.

“Damuwata yanzu ita ce yadda za a saki sauran fasinjojin lafiya ba tare da lahanta kowanne ba,” in ji Buhari.

Dangane da umarnin da ya bai wa rundunonin tsaron kasar a baya-bayan nan kan kawo karshen ayyukan ta’addanci a Najeriya kuwa, shugaban ya ce rahotanni da ke ishe shi a ’yan kwanakin nan na nuna suna bin umarnin nasa sau da kafa.