Abin da ke kai ni wurin dan bindiga yana lalata da ni —Matar aure | Aminiya

Abin da ke kai ni wurin dan bindiga yana lalata da ni —Matar aure

    Aliyu Babankarfi, Zariya

Wata matar aure da ke zuwa wajen wani dan bindiga yana lalata da ita ta ce gudun kada a kashe iyayenta ne ya sa ta ba shi kanta.

Matar da ke zaune a kauyen Tankarau a yankin Madaci da ke Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna ta ce sunan dan fashin bindigar da take zuwa wurinshi yana lalata da ita Idi Dan Ibrahim.

Ta ce,”Tun da nake zuwa wajen dan bindigar ya yi lalata da ita sau daya ya taba ba ta N5,000 daga baya idan ta je, ba ta yarda da shi, in mishi ba ni da da lafiya ko ina jini, don haka sai ya daina ba ni komai.”

Ta ce bayan kama ta ta shiga damuwa saboda mijinta da ’ya’yanta duk sun shiga damuwa saboda ganin halin da ta shiga.

Yanzu haka tana hannun jami’an tsaro na IRT kafin kammala bincike.