✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya kawo tsaiko a Shari’ar Ganduje

Ana zargin su da laifuka takwas na zargin karɓar rashawa, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati

Rashin bayar da sammaci ga tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da matarsa da dansa da wasu mutane biyar ya kawo tsako ga shirin da gwamnatin Kano ta yi na gurfanar da su.

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 4 karkashin jagorancin Mai sharia Usman Na’abba ita ce ta sanya wannan rana domin gurfanar da su Ganduje.

Gwamnatin Kano ta yi karar tsohon gwamnan ne bisa tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da zargin karɓar cin hanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da kadarorin gwamnati.

Sauran wadanda ake karar sun hada da matarsa Hafsat Umar da wasu mutane da suka hada da Abubakar Bawuro da Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad da Kamfanin Lamash Properties Ltd da Kamfanin Safari Textiles Ltd da kuma Kamfanin Lesage General Enterprises.

Gwamnatin Kano ta ce ta tanadi shaidu 15 da za su bayyana a gaban kotu.

Masu gabatar da kara lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa ba su sami damar bayar da sammaci ga wadanda ake kara ba saboda wasu daillai.

Sun yi kokarin kotun ta ba su damar bayar da sammaci ga wadanda ake kara ta wasu hanyoyin daban.

Sai dai Barista Nuraini Jimoh wanda shi ne lauyan kariya ga wanda ake kara na shida Kamfanin Lamash ya soki rokon masu, inda ya kafa hujja da cewa a shari’a ta laifi ba a bayar da sammaci ta yin amfani da wasu kafofin sai dai hannu da hannu.

Alkalin kotun Mai sharia Usman Na’abba ya bayar da a sake mika wa wadanda ake kara sammaci sannan kotun ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu, 2024.