✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa aka ture Shekau a shugabancin Boko Haram

Tun lokacin da kungiyar  ISIS ta sanar a ranar 3 ga watan Agusta cewa Abu Musab Albarnawi ne sabon kwamandanta na yankin Afirka ta yamma,…

Tun lokacin da kungiyar  ISIS ta sanar a ranar 3 ga watan Agusta cewa Abu Musab Albarnawi ne sabon kwamandanta na yankin Afirka ta yamma, bayan tsige Abubakar Shekau, wanda shi ne ya sanar da cewa suna mubaya’a ga kuniyar ta ISIS a shekarar 2015, sai rikici ya fara bayyana.
Shi dai Abu Musab Albarnawi da ne na wanda ya kirkiro gunyiyar Boko Haram watau Muhammad Yusuf, wanda jami’an tsaro suka kashe a shekarar 2009 a Maiduguri da ke Jihar Borno, jim kadan bayan’yan kungiyar sun yi tawaye.
Mintoci kadan bayan sanarwar da ISIS fitar, sai shi ma Shekau ya saki wani faifen bidiyo inda ya ce Abu Musab Albarnawi kafiri ne, wanda hakan ya sa masu sharhi suke ganin cewa Shekau yayi tawaye ga shugabancin ISIS na yankin.
Lamarin ya bude sabon shafi a kan rikicin cikin gida da kungiyar Boko Haram take fama da shi a kwanakin nan, ganin yadda wadansu daga cikin mayakan Boko Haram suke zargin Shekau da kisan gilla da kuma cewa ya kauce daga asalin manufar jihadi da kuma akidu da sauransu.
Bayanin Shekau ya nuna cewa babu mamaki ya yi amfani da karfinsa domin ya fuskanci Albarnawi da mabiyansa da yaki, wanda ake sa ran idan jami’an tsaro na hadin gwiwa (MNJTF)da  suka hada da kasashen Chadi da Kamaru da Najeriya da Nijar suka kula da kyau zai taimaka musu wurin murkushe ‘yan ta’addan.
Shekau ya bayyana cewa, “ mun ji wani labari na yawo kuma ana danganta shi da  kungiyar ISIS wanda muka yi wa mubaya’a  a baya, duk da cewa ba wai ba ma tare da su ba ne, muna nan a kan akidarmu. Mun san inda muke da bambanci, sannan kuma na rubuta musu takarda a kan wannan da dadewa. Duk abin da muka rubuta yana nan a ajiye, wani shafuka takwas ne, wani kuma shafuka tara ne. Ina so duniya ta san cewa muna nan a kan akidarmu, sannan kuma muna tare da Alkur’ani, ba za mu yi tawaye ba, za mu tsaya a kan hanyar Allah. da’a ga Manzon Allah Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) dole ne, kuma za mu cigaba da binsa har karshen lokaci.’’ Inji shi.
Shekau ya kara da cewa, an ci amanarsa sannan kuma an yaudari shugabancin ISIS ne wurin yanke shawarar tsige shi, “wannan shi ne matsayarmu, sannan kuma muna nan a matsayinmu na Jama’atu Ahlussunna Lidda’awati Waljihad,” inji shi, inda yake jawabi da harsunan larabci da Hausa.
kungiyar ISIS a shafinta na yanar gizo ta sanar da cewa Abu Musab Albarnawi shi ne sabon wakilinta na yankin Afirka ta yamma, sannan kuma ba ta ambaci sunan Shekau ba a cikin sanarwar. Sabon shugaban yana amfani da alkunya da sunan dansa Musab,, wanda ake tunanin dan shekara 7 ne wanda kuma jika ne a wurin marigayi Muhammad Yusuf.
Muhammad Yusuf ya rasu ne a shekarar 2019 yana dan shekara 39, yawancin shugabannin Boko Haram suna amfani da suna na alkunya ne a maimakon sunayensu na ainihi, inda wadansu suke jingina sunansu ga iyayensu, wadansu kuma suke jingina sunansu ga ‘ya’yansu, kamar Abu Isa, wanda yake nufin baban Isa, ko kuma Ibn Muhammad Albarnawi, wanda yake nufin dan Muhammad daga Borno.
Bincike ya nuna cewa Abu Musab Albarnawi yana dan karami ne lokacin da aka kashe mahaifinsa Muhammad Yusuf. Bayan rasuwar  mahaifinsa, sai Shekau da wani Mamman Nur suka raine shi har zuwa yanzu da yake da shekaru ashirin da ‘yan kai.
Musab Albarnawi an ce ya samu ilimin Alkur’ani sosai da kuma ilimin Fikhu kuma ya fahimci irin ayyukan tayar da kayar bayan da ake yi a yankin Gabas ta tsakiya, wadda ta haka ne aka tsara hanyar da ta fito da shi har ya shahara.
Lokacin da Muhammad Yusuf yake raye Shekau ne mataimakinsa na farko, sai Mamman Nur, da Khalid Albarnawi ,wanda aka kama shi a Lakwaja da ke Jihar Kogi a ranar Juma’a 1 ga watan Aprailu na shekarar 2016.
Amma, ana tunanin jim kadan bayan rasuwar MuhammadYusuf, Shekau da Mamman Nur sun samu sabanin ra’ayi, wanda hakan ya sa Mamman Nur ya fice daga sansanin, sannan kuma ya jagoranci kafa kungiyar  Ansaru, wadda ta yi fice wurin sace mutane ‘yan kasashen waje.
Hakan ya sa Khalid Albarnawi (wanda yake hannun jami’an tsaro yanzu) ya zama na biyu a sansanin da ke karkashin Shekau bayan ficewar Mamman Nur.
Ana tunanin shi dan Muhammad Yusuf din zai cigaba da kasancewa a karkashin kulawar Shekau, amma bayan ya fara girma, kuma ya samu ilimi, sai ya fara damuwa da yadda Shekau yake kashe wadanda aka kama da kuma mabiyansa ba tare da nuna tausayi ba.
Bayan Shekau ya yi mubaya’a ga kungiyar ISIS a ranar  5 ga watan Maris ta shekarar 2015, an ce an sulhunta tsakaninsa da Mamman Nur, wanda shi kuma yana da alaka da kungiyoyin ta’addanci da dama a duniya, amma duk da haka haduwarsu ba ta yi daidai ba, wanda hakan ya sa Mamman Nur ya kara ficewa daga sansanin da ke karkashin Shekau tare da wadansu mabiya masu yawa, cikinsu har da Abu Musab Albarnawi.
“Kamata ya yi Mamman Nur ya zama sabon shugaba a yankin Afirka ta yamma, amma saboda wadansu dalilai sai ya ce ya bar wa dan Muhammad Yusuf shugabancin,” inji wani majiya da ke kusa da kungiyar.
Wannan lamarin ya nuna cewa Ansaru ta samu nasara a kan Boko Haram, ko kuma a ce Mamman Nur ya samu nasara a kan Shekau. Duk da cewa lamarin ya jefa Boko Haram cikin rikici wanda kuma zai taimaka wa jami’an tsaro, wadanda suka san kungiyar sosai sun ce har yanzu Shekau yana da karfi sosai kuma yana da makamai masu yawa. Haka nan kuma  ‘yan matan Chibok  sama da dari biyu wadanda aka sace a watan Aprailu na shekara 2014 suna wurinsa, amma kuma ana tunanin wadansu ‘yan matan suna wurin Abu Musab Albarnawi da mabiyansa.
Don haka, gwamnatin Najeriya ya kamata ta nemo yadda za ta yi da karbo ‘yan matan, wanda shi ne ake ganin babbar nasara a kan kungiyar Boko Haram.
Ana tunanin cewa sansanin Shekau da na Abu Musab Albarnawi suna kusa, babu nisa tsakaninsu a yankin tafkin Chadi, duk da cewa ana tunanin Shekau yana da wani sansanin a cikin dajin Sambisa, inda ya ajiye ‘yan matan Chibok da wadansu wadanda aka sato, wadanda suka hada da maza da mata da kuma wadansu daga cikin mayakansa.
Mamman Nur shi ne wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai wa ofishin Majalisar dinkin duniya da ke Abuja a watan Agusta na shekarar 2011, wanda hakan ya sa  kasar Amurka ta ayyana shi a matsayin dan ta’addan duniya.
Duk da cewa daga yanzu Abu Musab Albarnawi shi ne shugaban Boko Haram ko kuma wakilin ISIS na yankin Afrika ta yamma, amma Mamman Nur ne zai ja ragamar kungiyar. Masana suna ganin maganar cewa wai sabon shugaban ba zai kai hari masallatai da kuma wuraren tarukan mutane ba yaudara ce kawai, domin kuwa ita kanta kungiyar ISIS wacce yake wakilta tana aikata irin wadannan kisan kiyashin.