✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da rikicin Rasha da Ukraine

Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da tankiyar da ke ci gaba da faruwa.

Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO ta aike da karin dakarunta zuwa Kyiv, babban birnin Ukraine saboda shirin ko-ta-kwana, a daidai lokacin da kasar Rasha ke ci gaba da jibge dakarunta a kan iyakarta da Ukraine.

Rasha dai ta ce daukar matakin ya zamar mata wajibi don ta kare muradunta, musamman la’akari da yadda ta ce kungiyar ta NATO na neman yi wa zaman lafiyar yankin barazana.

Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da tankiyar da ke ci gaba da faruwa a yankin.

Meye musabbabin rikicin?

Kafin rugujewar Tarayyar Soviet dai a shekarar 1991, Ukraine wani bangare ce a tarayyar, kuma ta samu ’yancin kanta ne bayan rugujewar.

Sai dai tun bayan lokacin, kasar ta yi watsi da akasarin manufofin Rasha, inda ta fi mayar da hankalinta ga kasashen Yamma.

Wani yunkuri da tsohon Shugaban Kasar ta Ukraine, Viktor Yanukovych ya taba yi na juya wa Tarayyar Turai baya don goyon bayan Rasha ya fuskanci mummunar zanga-zanga, wacce daga bisani kuma ta yi awon gaba da kujerarsa a shekarar 2014.

Rasha dai a lokacin ta mayar da martani ta hanyar mamaye wani bangare na Ukraine mai suna Crimea, sannan ta ci gaba da taimaka wa ’yan tawayen kasar.

Bugu da kari, Rasha ta sha zargin Amurka da kawayenta na NATO da tallafa wa Ukraine da makamai, inda ta yi gargadin cewa duk wani yunkuri na shigar da Ukraine cikin kungiyar zai kara zaman dar-dar a yankin.

Takamaimai me Rasha take nema?

Takamaimai dai kasar Rasha ba ta so Ukraine ta shiga kungiyar NATO, sannan tana son kungiyar ta NATO ta janye daga Gabashin Turai sannan ta daina yin atisaye a kusa da kasarta.

Shugaban Rasha, Vladimir Putin dai ya sha neman a samu tsayayyar tattaunawa ba wai kawai ta fatar baki ba, har ma da wacce za ta magance kowacce irin barazana.

Kafin dai NATO ta amince da shigar Ukraine cikinta, dole ne sai daukacin mambobin kasashe 30 na cikinta sun amince da bukatar hakan.

Shin Ukraine za ta shiga NATO?

Kasar Ukraine dai ba mambar NATO ba ce, amma tana hankoron shiga cikinta, ko da yake ana yi mata kallon kawar kungiyar.

Babban Magatakardar NATO, Jens Stoltenberg, ya fada a watan Disambar 2021 cewa yunkurin Rasha na dakatar da Ukraine daga shiga kungiyar tun shekarar 2008, wata rana zai zama tarihi.

Jens dai ya ce idan lokacin tabbatar da hakan ya yi, ko shawara ba za su tsaya yi da Rasha ba.

Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun ce mambobin NATO, musamman Amurka na jan kafa a kan amincewa Ukraine ta shiga kawancen saboda gudun kada su lalata alakarsu da Rasha.

Akwai yuwuwar fafata yaki ne?

Kasashen Yamma dai na zargin Rasha da jibge dakaru 10,000 a kan iyakarta da Ukraine, a shirye-shiryen da take yin a mamaye kasar.

Shugaban Amurka, Joe Biden dai ya yi gargadin cewa Rasha za ta dandana kudarta muddin ta kuskura ta mamaye Ukraine din.

Tuni dai hukumar tsaron Amurka ta PENTAGON ta ce ta ware sojoji 8,500 saboda jiran ko-ta-kwana a yankin na Gabashin Turai, kafin daga bisani ta aike da karin jiragen ruwa na yaki da na sama zuwa yankin.

Sai dai a cewar kakakin Shugaba Putin, barazanar kawai za ta kara zaman dar-dar din da ake fama da ita ne a yankin.

Rasha dai ta musanta cewa tana kokarin mamaye Ukraine ne, sannan ta zargi kasashen Yamma da zuzuta wutar rikicin.

Sai dai babu tabbacin ko kasashen biyu za su fafata yaki da juna a kan lamarin.

Me zai faru idan Rasha ta mamaye Ukraine?

Kasashen Yamma da dama dai sun bayyana goyon bayansu ga Ukraine, inda Birtaniya ta aike da makamai, Jamus kuma za ta aike da jami’an lafiya zuwa karshen watan Fabrairu.

Ana kuma ci gaba da tattaunawa kan yadda za a kakaba wa kasar takunkumi.

Tuni dai kasar Amurka da takwarorinta na Turai suka yi barazanar kakaba takunkumin karya tattalin arziki muddin Rasha ba ta janye aniyar tata ba.

Sai dai masana tattalin arziki na harsashen cewa matukar aka dauki matakin hana hada-hadar kudade tsakanin bankunan kasar da sauran na kasashen duniya, matakin zai yi mummunar illa ga tattalin arzikinta.

Amurka dai, wacce ke da daya daga cikin abubuwan da ke juya tattalin arzikin duniya (Dala) za ta iya hana Rasha amfani da ita dungurungum.