✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da aka yi rangwame a kansu da azumi

Allah Ya kare mu Ya ba mu dacewa.

Yana daga cikin sauki na wannan shari’a ta Musulunci yin rangwame a kan wasu abubuwa da za su iya bijirowa a lokacin ibada.

Haka shi ma mai azumi akwai abubuwan da aka yi masa rangwame a kansu.

Daga ciki akwai:

Idan mai azumi ya ci ko ya sha cikin mantuwa, ko wani abu ya wuce zuwa makoshinsa daga abubuwan da suke warware azumi, an yi masa rangwame kuma azuminsa yana nan bai baci ba, saboda fadin Manzon Allah (S.A.W) cewa: “Idan mai azumi ya manta ya ci ko ya sha, to ya karasa azuminsa, domin Allah ne Ya ciyar da shi Ya shayar da shi.”

Da fadin Manzon Allah (S.A.W) cewa: “Allah Ya yi yafiya ga al’ummata cikin abin da suka yi na kuskure, ko mantuwa, ko abin da aka tilasta su suka aikata.”

Idan mai azumi ya jahilci lokacin buda-baki ko lokacin sahur, sai ya yi buda-baki kafin faduwar rana ko ya yi sahur bayan kiran Sallah, shi ma an yi masa rangwame, saboda fadin Allah: “Babu laifi a kanku cikin abin da kuka yi kuskure…” (Ahzab: 1).

Idan mai azumi ya yi amai ba da gangan ba shi ma an yafe masa, amma idan da gangan ya kakaro aman to azuminsa ya lalace.

Rinjayar hadiyar wani kwaro ko hayakin kan hanya ko kurar da ba za a iya kauce mata ba, ko mai sana’ar siminti ko dakon kanwa, ko gari da duk abin da yake da alaka da wadannan abubuwan an yi rangwame a kansu.

Yin asuwaki

Ya halatta ga mai azumi ya yi asuwaki a kowane lokaci domin tsabtace bakinsa don kwadaitarwar Musulunci a kan tsabta, haka nan yin amfani da duk abin da zai kawar da dattin baki, kamar makilin da makamancinsa.

Kurkurar baki ko shakar ruwa ba tare da wuce iyaka ba, haka nan yi wa rauni aiki ko disa magani a kunne ko ido ko sa kwalli, ko amfani da turare, na fesawa ko turaren wuta, ko mutum ya wayi gari da janaba, ko yin mafarki da makamantansu, dukkan wadannan abubuwa an yi rangwame a kansu.

Abubuwan da suke vata azumi:

Abubuwan da suke bata azumi suna da dama daga cikinsu akwai:

  • Cin abinci ko shan abin sha da gangan ba tare da wani uziri ba a tsawon yini.
  • Yin jima’i a cikin yinin watan Ramadan yana lalata azumi, wanda duk ya yi sai ya rama kuma ya yi kaffara.
  • Kago amai da gangan yana lalata azumi.
  • Fitar da maniyyi da gangan ta kowace irin hanya yana lalata azumi.
  • Zuwan jinin al’ada ko na haihuwa yana lalata azumi.
  • Kakalo jini ta baki ko hanci ko kunne da gangan shi ma yana lalata azumi.
  • Ba da jini in dai ba ya zama akwai larura mai karfi ba.

Wasu abubuwa da suka kamata a kula da su:

Na farko: Mutumin da yake azumi amma yana sakaci da Sallah.

Wadansu suna kokarin himmatuwa wajen yin azumi da yin Tahajjudi a cikin watan Ramadan amma suna sakaci da yin sallolin farilla, wadansu ma ba su yin sallar kwata-kwata, bisa ga wannan malamai sun yi bayanai kamar haka:

(1). Mutumin da ba ya Sallah kwata-kwata da gangan suna ganin cewa ya kafirta, domin Sallah ita ce ginshikin addini, saboda haka wanda yake cikin wannan hali ko ya yi azumi, to azuminsa bai inganta ba.

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Alkawarin da ya bambantamu da su (Yahudu da Nasara), Shi ne Sallah. Wanda ya bar ta to hakika ya kafirta.”

Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Babu abin da ya rabe tsakanin bawa da shirka sai barin Sallah duk wanda ya bar ta to hakika ya yi shirka.”

Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Tsakanin bawa da kafirci shi ne barin sallah.”

Bisa ga wadannan dalilai malamai suke ganin cewa mutumin da ba ya Sallah kwata-kwata da gangan to ya kafirta.

(2) Wanda ya bar Sallah da sakaci amma ya yarda da wajibcinta, to haqiqa ya yi babban laifi, amma azuminsa ya inganta da sauran ayyukansa na ibada amma al’amarinsa na ga Allah.

Ya wajaba mu sani cewa sha’anin Sallah abu ne mai girman gaske domin da ita ce bawa ke samun kusanci sosai zuwa ga Ubangijinsa, har ma Allah Ya wajabta wa bayinSa kiyaye ta inda Yake cewa: “Ku kiyaye salloli da Sallar Tsakiya, ku tsaya ga Allah kuna masu takawa.” (Baqara).

Kuma hakika Allah Ya tanadi azaba ga masu yin sakaci da Sallah, Allah Ya ce:“Azaba ta tabbata ga masallata wadanda suke yin sakaci a kan sallarsu.” (Al-Ma’un: 4-5).

Ya wajaba a wuyan Musulmi kiyayewa a kan sallolin nan guda biyar a cikin Ramadan ko wajen Ramadan, don kada ayyukan bawa su lalace ya kasance cikin asararru, kuma haqiqa Allah da Manzonsa (S.A.W) sun yi gargadi sosai tare da razanarwa ga masu yin sakaci da sallah, saboda masu barinta suna cikin hadari.

Babu makawa lallai barin Sallah da yin sakaci da ita da kin kiyaye ta a kan lokacinta da kuma kin yin ta cikin jama’a, na daga cikin kawar da kai daga ambaton Ubangiji da wulakantar da hukunce-hukuncenSa da zai iya janyo wa mai yin hakan azabar Ubangiji da nisanta daga rahamarSa.

Allah Ya kare mu Ya ba mu dacewa.

Matsayin Azumin Ramadan a Birnin Makkah

Abu ne sananne cewa yin Sallah a Haramin Makkah ya fi falala fiye da yin ta a wani waje, kuma yin ta a cikin Masallacin Haramin Makkah ya fi Sallah dubu 100 a wani waje na daban, saboda girma da matsayin dakin Allah.

Saboda kwadayin wannan falala da yawa daga cikin mutane suke zuwa wannan waje a cikin watan Ramada.

Don haka ya kamata mutane su sani cewa shi azumi ba ya da wani fifikon lada don an yi shi a Makka ko a wani waje, amma babu laifi ga wanda Allah Ya ba shi dama ya yi azuminsa na Ramadan a can saboda darajar wajen.

Dokta Ahmad Adam Kutubi (SP) Hedikwatar ’Yan sanda ta Zone 7, Wuse Zone 3, FCT, Abuja 08036095723, 07045472372