✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ku san manyan kusoshin Gwamnatin Taliban 6

Dan Mullah Omar, wanda ya kafa kungiyar kuma shugabanta na farko ne Ministan Tsaro.

Bayan kungiyar Taliban ta sanar da sunayen ministoci da wasu muhimman mukamai a sabuwar gwamnatinta a Afghanistan;

Ga abubuwan da za ya kamata ku sani game da masu rike da muhimman mukaman:

– Mohammad Hasan Akhmund – Firai Minista

Akhund shi ne shugaban Majalisar Jagorancin kungiyar Taliban, wato Rehbari Shura. 

Shi ne Ministan Harkokin waje na farko kuma  Mataimakin Firai Minista a tsohuwar gwamnatin Taliban na 1996-2001.

Kamar yawacin shugabannin kungiyar, ana martaba Akhund saboda kusancinsa da babban jagoran farko na kungiyar, Mullah Mohammad Omar.

Shi dan asalin Kandahar ne, mahaifar Taliban.

Wata majiya ta Taliban ta ce suna matukar girmama Akhund, musamman ma babban jagoran kungiyar, Haibatullah Akhundzada.

Bayan ga kasancewarsa shugaban addinin Taliban, Akhund mai shekaru akalla 60 jagoran siyasa ne da ke da iko a kan majalisar jagorancin kungiyar da kuma fada a ji a harkokin sojinta.

– Abdul Ghani Baradar – Mataimakin Firai Minista

Baradar babban amini ne ga Mullah Omar, wanda ya ba shi lakabin, ‘Baradar’ ko ‘dan uwana’.

Shi ne Mataimakin Ministan Tsaro a lokacin tsohuwar gwamnatin Taliban.

Bayan faduwar gwamnatin, Baradar ya zama babban kwamandan sojinta inda ya jagoranci kai wa sojojin hadin gwiwa hare-hare, inji sanarwar takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2010 an kama shi tare da tsare shi a Pakistan. 

Bayan sakin sa a 2018, shi ne ya jagoranci Ofishin Siyasa na Taliban a birnin Doha na kasar Qatar.

Ya  kuma kasance daya daga cikin fitattun mutane a tattaunawar zaman lafiya da Amurka.

– Amir Khat Muttaqi – Ministan Harkokin Waje

Muttaqi ya yi Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu da kuma Ministan Ilimi a tsohuwar gwamnatin Taliban.

Daga baya kungiyar ta tura shi zuwa Qatar inda aka nada shi mamba a Kwamitin Zaman Lafiya da tawagar tattaunawa da suka tattauna da Amurka.

Majiyoyi daga Taliban sun ce shi ba kwamandan yaki ba ne kuma ba shugaban addini ba.

Amma shi ne shugaban Hukumar Gayyata da Jagoranci, wanda ya jagoranci kokarin ganin jami’an gwamnatin kasar da manyan mutane su juya mata baya.

Wasu jawabai da ya yi ta yi a yayin da kungiyar ke kokarin kwace iko da kasar, ya nuna matsakaicin ra’ayi, yana kira ga rundunonin da aka jibge a cikin manyan larduna don tattaunawa da kungiyar don guje wa yaki a cikin birane.

Makwanni bayan Taliban ta kwace Kabul, Muttaqi ya taka irin wannan rawa a lardin Panjshir, inda ya yi kira da a sasanta da bangaren da suka yi wa kungiyar turjiya.

– Mullah Yaqoob Omar – Ministan Tsaro

Shi ne dan Mullah Omar, wanda ya kafa Taliban kuma ya nemi ya gaji mahaifinsa a shekarar 2015. 

Da farko ya fice daga taron majalisar jagoranci da ta nada Mullah Akhtar Mansour ya gaji Mullah Omar, amma daga baya aka sasanta.

Mullah Yaqoob Omar mai shekara 30 da ’yan kai ba shi da bai sai sauran manyan kwamandojin yaki na Taliban kwarewar gwagwarmaya ba.

Duk da haka yana samun gagarumar biyayya a yankin  Kandahar albarkacin martabar mahaifinsa.

A bara an nada shi a babban kwamandan sojin Taliban, wanda ke kula da duk ayyukan soji a Afghanistan.

Yana kuma daga cikin mataimakan shugabannin kungiyar uku, tare da Baradar da Sirajuddin Haqqani.

Aasu manazarta na Yammacin Turai na ganin yana da matsakaicin ra’ayi.

Amma kwamandojin Taliban sun ce yana cikin shugabannin da suka matsa a tsananta yakar biranen a cikin makonni kafin faduwar Kabul.

– Sirajuddin Haqqani – Ministan Harkokin Cikin Gida

Sirajuddin Haqqani, wanda sh ne Shugaban Cibiyar Sadarwa ta Haqqani mai tasiri, ya zama jagoranta ne bayan rasuwar mahaifinsa, Jalaluddin Haqqani, a 2018.

Da farko Amurka ta goyi bayansa a matsayin daya daga cikin manyan mayaka masu adawa da Tarayyar Soviet a shekarun 1980, an zargi kungiyar mai cin gashin kanta da wasu munanan hare-hare kan sojojin hadin gwiwa.

Cibiyar, wacce ake muhawara kan ainihin matsayinta a cikin tsarin Taliban, Amurka ta kira ta da Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Waje.

Kwamitin Takunkumin na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce kungiyar, wacce ke zaune a cikin iyakokin tsakanin Afghanistan da Pakistan, tana da alaka sosai a hakar safarar miyagun kwayoyi.

Haqqani yana daya daga cikin mutanen da FBI ke nema ruwa a jallo, saboda hannunsa a hare-haren kunar bakin wake da alaka da Al Qaeda. 

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya tukuicin Dala miliyan 10 ga duk wanda ya kai ga cafke shi.

– Zabihullah Mujahid – Mataimakin Ministan Yada Labarai

Shi ne kakakin kungiyar Taliban na tsawon lokaci.

Ya shafe sama da shekara 10 a matsayin mai magana da yawun kungiyar, yana wallafa bayanan ayyuuka da hare-haren kunar bakin waken kungiyar ta shafinsa na Twitter.

Ba a samu hotonsa ba sai bayan da ya gabatar da taron manema labarai na farko bayan kungiyar ta kwace Kabul a watan Agusta.

An kwashe shekaru da yawa jami’an leken asirin Amurka sun na zargin Mujahid suna ne kawai da mutane da yawa suke amfani da shi wajen gudanar da ayyukan watsa labarai na kungiyar.