✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Adadin mutanen da suka mutu a rugujewar benen Legas ya kai 36

A yau Alhamis an shiga kwanaki na hudu ana wannan aikin ceto.

A yayin da ake ci gaba da aiki ba dare ba rana wajen ceto mutanen da gini ya danne a Legas, ana samun karin gawarwaki inda a yanzu adadin wadanda suka mutu ya kai 36. 

Daga cikin mutum 36 da suka riga mu gidan gaskiya, akwai mata uku yayin da ragowar 33 duk suka kasance maza.

Shugaban Hukumar NEMA mai Ba da Agajin Gaggawa reshen yankin Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye wanda ya yi wannan karin haske, ya ce daga cikin wadanda aka ceto da suke da sauran numfashi a duniya, an samu mace daya da kuma maza takwas.

Hakan dai na zuwa ne yayin da a yau Alhamis aka shiga kwanaki na hudu ana wannan aikin ceto.

“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun kai ga matakin kasa,” in ji Farinloye, wanda ya kara da cewa an kawo manyan kayan aiki tun a yammacin ranar Talata domin gudanar da aikin.

Ana iya tuna cewa, da misalin karfe 2:45 na ranar Litinin ce wani bene mai hawa 22 ya ruguje a unguwar Ikoyi ta masu ido da kwalli da ke Jihar Lagos yayin da ake aikin gininsa.

Tun a wannan rana ce masu aikin ceto da wasu mazauna yankin suka shiga neman masu sauran numfashin karkashin baraguzai da karafa.