✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Adeleke ya sallami ma’aikata 12,000, ya sauke Sarakuna 3 a Osun

Sabon gwamnan ya ce an yi nade-naden ne ba bisa ka'ida ba.

Gwamnan Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya sallami ma’aikata 12,000 tare da kwance rawanin wasu sarakuna uku sa’o’i 24 bayan rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar.

Gwamnan ya kuma soke nadin Manyan Sakatarorin dindindin guda 30 tare da dakatar da shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Osun (OSIEC), Mista Segun Oladitan.

Sarakunan da abin ya shafa sun hada da Akinrun na Ikinrun Oba Yinusa Akadiri; Aree na Ire Oba Ademola Oluponle da Owa na Igbajo, Oba Gboyega Famodun.

Ya kuma umarci sarakunan da su fice daga masarautunsu, inda ya umarci jami’an tsaro su karbe ragamar masarautun.

Wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Adeleke, Olawale Rasheed ya fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa sabon Gwamnan ya sanya hannu kan umarnin zartar da dokokin da suka shafi batutuwan sarauta, batutuwan nade-nade, kafa kwamitin bita, tantance ma’aikata da kuma batutuwan daukar aiki.

Sanarwar ta ce: “Dukkan ayyukan da Gwamnatin Jihar Osun ta yi a kowane matsayi a cikin ma’aikatu, hukumomi, kwamitoci za a soke su.

“Dokar harkokin masarautu da nadin sarakunan gargajiya. Dukkanin nade-naden sarakunan gargajiya da gwamnatin Jihar Osun ta yi bayan ranar 17 ga Yuli, 2022, an ba da umarnin sake duba su don tabbatar da bin ka’idojin da suka dace na ayyana sarautun da kuma Dokokin Kasa da suka shafi masarautun.

“Dangane da batun Ikirun, Iree da Igbajo, domin gudun tabarbarewar doka da oda, an dage nadin na Akinrun na Ikinrun, Aree na Ire da Owa na Igbajo.

“Bayan haka, fadar Akinrun na Ikirun, Aree na Iree da Owa za su kasance babu kowa a ciki, yayin da aka umarci jami’an tsaro da su dauki  tsare masarautun.”

Tsohon Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya dauki ma’aikata sama da 12,000 aiki sannan ya nada sakatarorin dindindin 30.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Osun, Tesleem Igbalaye ya fitar, ta kuma bayyana sauran mambobin hukumar zaben jihar da aka dakatar da suka hada da: Yusuf Oyeniran, Suibat Adubi, Prince Yinka Ajiboye, Abosede Omibeku, Dosu Gidigbi, da Wahab Adewoyin.

Ya kara da cewa dakatarwar na zuwa ne bayan korafe-korafe da dama da suka shafi almundahanar kudade, rashin aiki, rashin zuwa aiki da sauran ketare iyakoki.