✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2023: Yau Najeriya da Afirka ta Kudu za su goge raini

Cacar bakar diflomasiyya ta barke tsakanin kasashen biyu, wadanda wasansu kan kasance masu zafi

Yau ce ranar da za a goge raini tsakanin tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya da Bafana Bafana ta kasar Afirka ta Kudu a Wasan Kusa da na Karshe a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka na 2023 (AFCCON 2023) da ke gudana a kasar Kwaddibuwa.

Za a barje gumi a wasan hamayyan ne a birnin Bouaké, da misalin karfe 6 na yamma agogon Najeriya, a daidai lokacin da kasashen biyu suke neman goge raini a tsakaninsu a bangaren wasanni da harkar nishadi.

A shekaru 20 da suka gabata, kasashen biyu sun kara da suja sau 9, inda Najeriya ta samu nasara sau biyar, suka yi canjaras uku, sannan Afirka ta Kudu ta samu nasara sau daya.

Hakan kuwa na zuwa ne a yayin da ake cikin rashin tabbas game da ko babban dan wasan Super Eagles, kuma Gwarzon Dan Wasan Afirka, Victor Osimhen, zai  samu buga wannan muhimmin wa wasa, sakamakon rashin lafiya.

Zuwa lokacin kammala hada wannan labari dai babu wata sanarwa daga hukumar Super Egales game da makomar Osimhen a wasan.

Cacar bakar diflomasiyya

A halin da ake ciki dai wasan ya jawo cacar bakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, wadanda a tsawon lokaci wasansu kan kasance masu zafi, inda duk wadda ta samu nasara kan yi shagulgula.

Cacar bakan ta taso ne bayan ofishin jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu ya gargadi ’yan kasarsa da kada su jefa rayuwarsu cikin hadari wajen yin murna idan suka samu nasara, domin guje yiwuwar hare-haren kin jinin baki.

Ofishin jakadancin ya ce sanarwar na da muhimmanci, lura da barazanar da ake wa ’yan Najeriya a fakaice a soshiyal midiya, don haka su da su san inda za su je kallon wasan da kuma kiyaye harshensu idan suka samu nasara.

Kafin wasan dai wasu  ’yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu sun ce za su yi walima su raba abinci idan suka samu nasara a wasan.

A lokuta da dama, ’yan Najeriya sun sha fuskantar hare-hare har da kisa da sunan boren kin jinin baki daga al’ummar kasar Afirka ta Kudu.

Martanin Afirka ta Kudu

Sai dai kuma gwamnatin Afirka a Kudu ta soki gargadin da cewa ba shi da wani amfani, in banda ma haifar da fargaba na ba gaira babu dalili.

Sanarwar da ofishin harkokin wajen Afirka ta Kudu ta fitar da sanarwa cewa, “a tarihi, masoya kwallon kafan kasarmu ba su taba ta da rikici saboda wasansu da Najeriya ba.

“Mun yi imanin babu wata barazana da za su yi wa ’yan Najeriya kuma ba mu aminta da fargabar da ofishin jakadancin Najeriye ke nunawa game da al’ummarsa ba.”

Dambarwar kambin Grammy

A ranar Lahadi ne dai mawakiyar Afirka ta Kudu, tyla ta lashe kambin Grammy Gwarzuwar Mawakiyar Afirka, inda ta doke manyan mawakan Najeriya ciki har da Burna Boy da Davido da Ashake.

Idan Super Eagles samu nasara a wasan ranar Laraba, ’yan Najeriya na ganin hakan zai sa su huce haushinsu, kan rasa kambin Grammy da suke ganin tyla ba ta cancanta ba.

Sai dai kuma idan Afirka a Kudu ta doke Najeriya a wasan hamayyan, to ta yi wa Najeriya fintinkau ke nan da duka biyu a bangaren kwallon kafa da waka.