✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON: Super Eagles ta ɗinke rabuwar kai — Ahmed Musa

Ahmed Musa ya ce hadin kan tawagar ya ɗinke rabuwar kai da ake fama da ita a Najeriya.

Kyaftin din tawagar ‘yan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, ya bayyana cewar yana alfahari da tawagar duk da rashin nasara da suka yi a wasan karshe na Gasar AFCON ta 2023 a hannun Ivory Coast.

Ivory Coast, ta warware kwallon da Najeriya ta sanya a ragarta bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a filin wasa na Alassane Ouattara, da ke Abidjan, Babban Birnin Kasar.

Da yake martani game da wasan, Musa wanda bai buga ko wasa daya a gasar ba, ya ce tawagar ta ɗinke barakar rarrabuwar kai game da addini da kabilanci da ake fama da su a Najeriya.

Kyaftin din ya gode wa magoya bayan tawagar kan irin soyayyar da suka nuna musu yayin buga gasar da aka kammala a ranar Lahadi.

“Duba da irin rawar da muka taka, ina alfahari da Super Eagles. Duk da ba mu yi nasara ba amma hadin kanmu a cikin fili ya ɗinke rarrabuwar kan addini da kabilanci, hakan ya nuna karfin kwallon kafa.

“Muna godiya ga ‘yan Najeriya kan irin goyon bayan da suka ba mu. Mu ci gaba da hada kai don samun nasara a fili da kuma wajen fili,” a cewar Musa.

Super Eagles dai ta kare a mataki na biyu a gasar AFCON ta 2023, bayan shan kashi da ci 2 da 1 a hannun masu masaukin baki, kuma za su baro birnin Abidjan da yammacin ranar Litinin don dawowa Abuja.