✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin jarida na gaskiya yasa Media Trust karbuwa a Najeriya- Gwamnan Ekiti

Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya Dokta Kayode Fayemi, ya yabawa kamfanin rukunin jaridun Media Trust masu jaridar Aminiya, kan dagewa a kan…

Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya Dokta Kayode Fayemi, ya yabawa kamfanin rukunin jaridun Media Trust masu jaridar Aminiya, kan dagewa a kan aikin jarida na gaskiya, inda ya ce hakan yasa jaridun karbuwa a Najeriya baki daya.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin taron tattaunawa da aka shirya ta shekara-shekara da kamfanin ya gudanar yau Alhamis a Abuja karo na 17, ya ce bayaga kasancewar jaridar a gaba a yankin Arewa, haka nan ta samu karbuwa a sauran sassan Najeriya ciki harda yankinsa na Kudu maso Yamma, inda ke matsayin cibiyar jaridun Najeriya.

Tun farko a yayin kaddamar da taron, shugaban kwamitin amintattu na kamfanin, Malam Kabiru Yusuf ya bukaci masu gabatar da mukala a taron da su maida hankali wajen samar da maslaha a kan tsarin mulkin dimokuradiyyar kasar nan, da a yanzu ta cika shekara 20, wanda shi ne taken taron na bana.

Sauran wadanda suka gabatar da jawabin sun hada da ’yar majalisar wakilai ta tarayya Lynda Chuba Ikpeazu, sai kuma sanata Sabi Abdullahi da ya wakilci shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, da ke matsayin shugaban taron.

Lynda Chuba Ikpeazu