✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai gwamnonin da suka nemi wa’adin mulki na uku — Obasanjo

Ba ni kadai na bukaci wa’adi na 3 kamar yadda ake ta yayatawa ba.

Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanja, ya ce gwamnonin da ya yi aiki da su zamanin mulkinsa su ma sun nemi a sauya Kundin Tsarin Mulki domin ba su damar zarcewa a karagar mulki.

Saboda haka Obasanjo ya ce ba shi kadai ya bukaci wa’adi na 3 kamar yadda ake ta yayatawa ba.

Obasanjo wanda ya dade yana watsi da zargin da ake masa na neman wa’adi na 3 da Majalisar Dokoki ta yi fatali da shi, ya zargi gwamnonin jihohi a lokacin mulkinsa a matsayin wadanda suka kitsa sauya Kundin Tsarin Mulkin wanda bai samu nasara ba.

Tsohon shugaban ya ce a wancan lokaci, gwamnonin jihohin na nuna cewar shi suke nemawa damar yin tazarcen, amma kuma gaskiyar maganar ita ce nemawa kansu suke yi domin da zarar majalisa ta amince da bukatar, su ma sun samu damar da suke bukata kenan.

Yunkurin sauya Kundin Tsarin Mulkin a shekarar 2006 ya samu koma baya lokacin da Majalisar Dokokin Tarayya a karkashin shugabanta, Ken Nnamani ta yi fatali da bukatar.

Nnamani ya shaida wa manema labarai cewar sun dauki matakin ne domin kare dimokuradiyar Najeriya ta hanyar sadaukar da mukamansu na siyasa saboda tabbacin da suke da shi cewar shugaba Obasanjo zai musu bita kulli saboda hana shi damar zarcewa.