✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai rashin tausayi a ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnati ta yi — NLC

Wata alama ce da ke nuna cewa jin daɗi da walwalar ’yan Najeriya ba shi da muhimmanci a wurin gwamnati.

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da waɗansu kungiyoyin fararen hula sun yi tir da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da tsarin wuta mai daraja ta ɗaya wato Band A.

A zantawarmu da wasu daga cikin ’yan rajin kawo canji da kuma ’ya’yan kungiyar NLC, sun ce duk dalilan da jami’an gwamnati suka bayar kan karin kudin ba hujjoji ba ne.

A cewarsu, ko a ƙasashen da aka ci gaba, ana tallafa wa wasu ɓangarori kamar man fetur da wutar lantarki.

A jiya Laraba ce dai Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da ƙarin kuɗin kilowatt na wuta daga Naira 68 zuwa N225.

Wannan karin ga masu amfani  da tsarin Band A da ke samu wuta na tsawon sa’o’i 20 a kullum za su riƙa biyan N135,000 kowane wata.

A taron da mataimakin shugaban NERC, Musiliu Oseni ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce karin zai shafi kaso 15 na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 a Najeriya.

Za Mu Ɗauki Matsaya — NLC

Shugaban yada labarai a hedikwatar NLC, Benson Upah, ya ce Ƙungiyar ta su za ta ɗauki matsaya kan mummunan ta’asar da aka yi na ƙarin kuɗin wuta.

Benson ya ce, za su sanar da matsayarsu idan masu ruwa da tsaki a kungiyar sun zauna.

“Shawarar da gwamnati ta yanke ba iya rashin tausayi ba ne, shawarace mai muni ƙwarai da gaske.”

Ya ce “wannan hukunci zai ƙara wa ’yan Najeriya wahalar da suke ciki. Sannan kuma zai ƙara gigita harkokin kasuwanci a ƙasar nan.

“Abin da in aka yi wasa zai kore masu saka hannun jari daga ƙasashen ƙetare a Najeriya.

Ya kara da cewa, “Mutanen da za su ci riba daga wannan tashin hankali da jama’a za su shiga su ne Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF.

“Abin tausayi! Za mu dawo gare ku a kan wannan batun nan gaba kaɗan, bayan masu ruwa da tsaki a kan wannan mataki na ƙungiyarmu sun zauna.”

Kungiyoyin Fararen Hula Sun Yi Martani

Babban Daraktan Cibiyar Kula da ‘Yancin Bil Adama da Ilimin Jama’a (CHRICED), Kwamared Ibrahim Zikirullahi, ya yi kakkausar martani ga Gwamnatin Tarayya kan ƙarin kuɗin wutan lantarki ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba,

Ya ce, “a halin da muke ciki a ƙasar nan, musamman dangane da irin wahalar da ake fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur, da kuma kasa dawo da darajar Naira, cire tallafi a ɓangare wutar lantarki wata alama ce da ke nuna cewa jin daɗi da walwalar ’yan Najeriya ba shi da muhimmanci a wurin gwamnati.”

A nasa bangaren, daraktan kungiyar ActionAid Nigeria, Andrew Mamedu, ya ce “karin wani ƙarin nauyi ne mai wuyar sauke wa aka dora a wuyan ’yan Najeriya, musamman masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu kananan sana’o’ii.

Karin Kuɗin Zai Janyo Satar Wutar Lantarki 

Wani tsohon shugaban NERC, Sam Amadi, ya ce ƙarin kuɗin wutar lantarki zai haifar da satar wutar kuma zai karfafa rashawa da almundahana a sashen.

Da yake magana a gidan Talabijin na Trust, Amadi ya ce, “Idan ka ƙara kudin wutar lantarki zuwa matakin da mutane ba za su iya ba, hakan zai ƙara janyo satar wuta ta bayan fage, cin hanci da rashawa, kuma a ƙarshe, ma’aikatu za su yi asara fiye da kima.

Sannan kuma, “eh gaskiya ne akwai kwakkwaran dalili na ƙara kuɗin harajin saboda matsalar kuɗin da ake samu da kuma karin farashin iskar gas da za a sayar wa kamfanonin samar da wutar lantarki.”