✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar mace ta zama Gwamnan Kaduna —El-Rufai

Gwamnan ya ce mata na da muhimmiyar rawa da za su taka a fagen shugabancin jihar.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce yana fatan mace ta zama gwamnar jihar, duba da irin yadda suke kara bunkasa harkokin yau da kullum.

El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya kara da cewa akwai yiwuwar mace ta zama gwamnar jihar saboda yawan da suke da shi a jihar.

Gwamnan, wanda mataimakiyarsa mace ce, Dokta Hadiza Balarabe, ya ce zai ci gaba da bai wa mata hadin kai da goyon baya a dukkanin matakai.

“Ba za ka mance da kashi 50 na jama’arka ba; wato ka yi tafi da hannu daya ke nan; kashi 50 cikin 100 na mata da matasan jihar nan mata ne.

“Mun tabbata bai wa mace dama irin ta maza zai ba su kwarin gwiwa su yi aiki tukuru fiye da maza.

“Mun zakulo mata mun ba su mukamai kuma ba su ba mu kunya ba, sun yi abin da ake so wajen ciyar da Jihar Kaduna gaba.

“Don haka muna tunanin fadin kasar nan su dauki darasin bai wa mata da matasa dama, don ita ce mafita wajen ciyar da kasa gaba,” a cewarsa.

Gwamnan ya kara da cewa, jihar na fatan samun mutum nagartacce da zai dora kyawawan ayyuka da ya zai bari.

“Za ta iya yiwuwa da wanda nake so, amma fatana shi ne zabi mafi alheri ga mutanen Kaduna, don haka ina so mu yi addu’a Allah Ya fito mana da na gari.

“Muna neman zabin Allah ga Jihar Kaduna, nagartaccen namiji ko mace da za su bunkasa rayuwar al’umma, sannan su gyara kura-kuran da na yi, su kuma ciyar da jihar gaba,” inji shi.