✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta intanet za a yanke hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Jamia'n tsaro sun ce ba su san inda alkalan kotun suke ba, kuma da alama ba za su halarci zaman da kansu ba

Wata kwakkwarar majiyar  tsaro ta shaida wa Aminiya a Kotun da za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano cewa har yanzu ba su san inda alkalan kotun suke ba, kuma da alamar ba za zo zaman da kansu ba.

Majiyar ta ce akwai yiwuwar alkalan za su halarci zaman ne ta bidiyo ta intanet, su kuma yanke hukunci, bisa umarnin da suka samu daga sama, saboda wasu dalilai na tsaro.

Hakan na zuwa ne a yayin da ake yi ta tayar da jijiyar wuya a harabar kotun, bayan jami’an tsaro sun shaida wa bangarorin da ke shari’ar cewa mutum 50 kacal, ciki har da su da ‘yan jarida da lauyoyi kadai aka amince su shiga cikin kotun.

Aminiya ta kawo rahoton yadda aka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da kewaye domin tabbatar da doka da oda.