Allah Ka yi mana magani. Shugaba Buhari kunnenka nawa? (3) | Aminiya

 Allah Ka yi mana magani. Shugaba Buhari kunnenka nawa? (3)

    Ibrahim Malumfashi

Ni abin da ya fi damuna game da irin da halin da ka samu kanka a halin yanzu shi ne na rashin sanin ina aka nufa, me za a yi, yaya za a yi, da kuma matakan da suka dace su kasance madafun da za ka yi amfani da su domin kai wa ga tudun-mun-tsira. Ina kuma jin wannan bai rasa nasaba da yadda ka shiga siyasar da dagwalon da ka bi ka kai ga matsayin da kake a yau. Na san ka sani, idan ba don hadakar jam’iyyarka ta CPC da ANPP da ACN da aka yi a ran 6 ga watan Fabrairun 2013 da kila ba ka kai labari ba, ganin cewa ka daura gyauto don kokowar samun shugabancin kasar nan a baya, akalla sau uku, amma ba a samu ba. Da kuma ka samu wannan damar, na san wannan tsarin ya yi maka dabaibayi, da ya hana maka yin irin yadda ka so, a lokacin da ka so. Ke nan tsarin jam’iyya da dimokuradiyya, ya Shugaba Buhari! Da alama bai yi maka kwalliyar da kai da kuma yawancin mutanen da ke matukar sha’awar ka kai ga wannan mulki ko matsayi ke bukata ba. Idan na ce ka samu kanka a matsayin wanda ke bisa turbar gaba-kura-baya-siyaki, ina jin ban yi kuskure ba. Kuma wannan ita ce matsalar, duk kuwa da cewa akwai babbar matsalar da ta fi ta, wadda kai ne, asasi kuma kai ne ta shafa kai-tsaye ba wai tsarin da ake gudanarwa ba, shi ma zan karaso gabar nan gaba. Ina mafita?

Bari in soma da batun tsarin jam’iyya da dimokuradiyya da na yi a baya. A matsayinka na tsohon soja, wanda ya yi mulki irin na kama-karya a zamanin mulkin da ba ruwansa da dimokuradiyya, na san ka yi amanna cewa za ka iya kamawa ka karya a wannan sabon tsarin shugabancin naka, idan damar hakan ta samu, amma da tafiya ta yi nisa ne kila ka gane cewa ashe rawar ba ta daka tsalle ba ce, ta tsayuwa ce, ana dan juyawa, a kuma daidai wannan lokaci ba yadda za a yi a zauna a ki taka rawar, shi ya sa aka shiga mirginawa ko da yaya ne, a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019.

To amma Mai girma Shugaban Kasa, kana jin wannan kadai ya isa hujjar da za mu ce komai ya ji dangane da wannan tafiya da aka yi a baya? Shin rashin zamanka wuka da nama a tsarin shugabancin kasar nan shi ne dalilin hana ka yin katabus daga wancan lokaci zuwa yau? Bayan zaben Shugaban Kasa da aka yi a 2019, inda ka sake samun nasara da gwaggwaban rinjaye, shin rawar ta canja zane? Shin dole sai ka yi shugabanci irin na soja ko na kama-karya ne za a samu nasarar bajen kolin ci gaban kasa? Shin gaskiya ne cewa ’yan Majalisar Tarayya ne da suke tadiye ka, ya hana maka famfalawa da gudu a daidai wancan lokaci zuwa yau? Da kuma aka yi watsi da waccan majalisa ta su Saraki, me ke jawo tafiyar hawainiyar kuma yanzu? Shin da gaske ne cewa kana ta kokarin motsawa, amma, wadansu ne da ba sa son mulkinka suka hana maka sakat, shi ya sa abubuwa uku da gwamnatinka ta yi niyyar aiwatarwa don ci gaban kasa; wato tabbatar da tsaro da tayar da komadar tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da almundahana suka gagara kawarwa ko samarwa? Shin hujjojin da masu bibiyar mulkinka, musamman masu mutuwar sonka da tsarin mulkinka suke bayarwa na cewa laifin ba naka ba ne, na wadansu ne, shin hakan gaskiya ne? Ina tabbatar maka ba gaskiya ba ce, bisa dukkan alkalumman adalci da za a yi amfani da su.

Ba kamar sauran masu nazarin tsarin mulkinka da kuma yadda kake gudanar da shi ba, ni ina da yakinin tabbas ka gaji kasa da gwamnati da tattalin arzikin da suke durkushewa ta kowace irin fuska mutum ya duba, musamman abin da ya shafi tattalin arzikin kasa da ya kasance cikin masassara dab da hawanka mulkin kasar nan, ka kuma yi iya kokari wajen ba shi kunun da ya sha ya fara farfadowa, amma ka sani, kamar yadda sauran al’umma ta sani, jinyar tattalin arzikin kasar nan yanzu ma aka fara, ba kuma wani abu ya hana a yi wa tattalin arzikin tiyata ba, sai rashin wani dabashiri domin fuskantar wannan kalubale. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba daga cikin wasu daliliai da ya wuce na rashin wani dawwamammen tsarin gina kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya dace, ba wai duba da bitar shifta daga littafin abin da Bankin Duniya ko Hukumar Lamuni ta Duniya suka bude maka ba. Ba tun yau ake fada ba, wadannan hukumomi, ba ’yan gatan kasashe irin Najeriya ne ba, ’yan gatan jari-hujja ne, ba talakawa da ke cikin kunci da damuwa ba a kasashen da ke tasowa a duniya ba. Na san za ka ce da ni ai an yi kokarin fitar da A’i daga sana’arta ta rogo a fagen tsarin tattalin arzikin kasar nan, ni kuwa sai in ce da kai, uwar kudin ma ba a fitar ba, balle kuma uwa-uba riba. Har yau A’i, wato talakawan Najeriya ba su ji ko gani ba, in kuwa sun ji da gani, to ba dai sauki ba, sai dai kunci da damuwa!

Ya Shugabana! Ba ina ganin wallenka ba ne a nan, matsalar ita ce, duk inda ka ji ana ta cewa sa-toka-sa-katsi, musamman a fagen gyaran tattalin arzikin kasa, to baba ne ya yi gardama. Matsalar tattalin arzikin kasar nan da yake some a halin yanzu a matakan ruhi ne da aiwatarwa in ana son a ga an kai ga gaci, ba matakan zama a ofis domin shan iska da dogon Turanci ba da muke gani a halin yanzu. Ga misali, gwamnatinka a cikin shekarun da ta yi tana mulki ta mayar da hankali ne wajen gine-gine da sassake-sassake da buge-buge da rushe-rushe, domin samar da hanyoyi ko jiragen kasa ko kwaskwarimar masana’antu da wasu kamfanoni da nome-nome don samar da amfanin gona da kayayyakin sarrafawa a kamfanoni da abincin ci, yin haka a tunanin gwamnatinka zai inganta farashin kayayyakin da ake sarrafawa da samarwa da kuma samun kudaden shiga a cikin kasa, domin a ci dunun dokin ci gaba, a kuma inganta komadar tattallin arziki ta fuskar (Madubin Tattalallen Ci gaban Kasa), GDP.

Za mu ci gaba