✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Almajiri ya zama miloniya a dalilin zobe

An tara masa kimanin Naira Miliyon 23.

Dare daya Allah kan yi bature in ji ’yan magana. Wannan ta tabbata a Jihar Kansas ta Amurka, inda wani maras galihu mai kwanan titi ya zama attajirin dare daya a samakon gaskiyar da ya aikata wanda haka ta sa jama’a ta tara masa Dala 150,000 kimanin Naira Miliyon 23.

Almajirin mai suna Billy Ray Harris na bara ne a bakin wata kasuwa a birnin Kansas ta kasar Amurka, bayan ya baro jiharsa ta Tedas domin neman na abinci biyo bayan korar sa da danginsa suka yi bisa dalilin cewa, sun daina ciyar da shi saboda ya zama ci-ma-zaune.

Cikin wannan hali ne wata mata mai suna Sarah Darling ta zo wucewa sai ta bude jakarta ta kuma dauko sadaka ta sa cikin kokon bararsa ta kuma yi tafiyarta.

Ashe a lokacin da take sa kudin zobenta mai adon lu’ulu’u ya sullube ya fada cikin kwanon ba tare da ta sani ba, inda ba ta ankara ba, sai da ta je gida.

Da ba ta ga zoben ba, sai ta dauka ta cire shi ta sa a jakarta ne, a inda ta zazzage jakar tare da fito da duk abin da ke ciki, amma ba ta ga zoben ba.

Da tabbatar da cewa zoben faduwa ya yi, sai hankalinta ya tashi. Gari na wayewa sai ta bi hanya, ta kuma koma wurin Billy, inda ta tambaye shi ko Allah Ya sa ya ga zoben nata mai tsada.

Billy ya sa hannu a aljihu ya fito da zobe ya mika mata, yana mai cewa, a cikin kokon bararsa ya gani, babu mamaki wurin ba shi sadaka ne a jiya ya fada ciki.

Wannan ya faranta wa Sarah rai matuka, bayan ta yi masa godiya cike da murna ta tafi gida, sai ta rika bayar da labarin abin da Billy mai bara ya yi na karamci, ta kuma kafa gidauniya a intanet na taimaka wa Billy tana mai kiran jama’a da su bayar da Dala daya kacal.

Hakan ya karde kasar, inda cikin dan kankanin lokaci aka tara wa Billy kimanin Naira miliyon 23. Kuma Sarah ta je ta mika wa Billy kudin, ba tare da rike ko kwabo ba.

Da aka kai wa Billy Harris kudin da farko kin karba ya yi, a inda ya ce ba zai karba ba, saboda bai cancanci kudin ba don kawai ya yi tsintuwa ya mayar wa da mai shi.

Daga karshe Billy ya karbi kudin ya kuma koma garinsu Tedas domin ya sayi gidan da zai zauna ya daina yawon bara.